Yajin Aikin ASUU: Ƙungiyar Daliban Najeriya Ta Yi Barazanar Fara Zanga-Zanga A Ƙasa

Yajin Aikin ASUU: Ƙungiyar Daliban Najeriya Ta Yi Barazanar Fara Zanga-Zanga A Ƙasa

  • Kungiyar daliban Najeriya ta kasa ta ba gwamnatin tarayya da kungiyar malamai ta kasa, ASUU wa’adi zuwa ranar 28 ga watan Maris akan su kawo karshen yajin aiki
  • NANS ta sanar da hakan ne ta wata takarda wacce ta saki a ranar Laraba ta shugaban ta, Sunday Ashefon inda yace matsawar ba a kawo karshen yajin aikin ba dalibai zasu fara zanga-zanga
  • A cewarsa dalibai daga jihohi 36 zasu fara bin titinan Abuja da katifu da kayan girke-girken su har sai gwamnati ta kawo mafita domin daidaitawa da ASUU

Kungiyar daliban Najeriya ta kasa, NANS ta ba gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami'o'i ta kasa, ASUU wa’adi zuwa ranar 28 ga watan Maris don su shirya da junayensu su kuma dakatar da yajin aiki.

Kara karanta wannan

Aiki kai tsaye ga masu 1st Class: Majalisa ta tattauna kan daukar masu digiri aiki

NANS ta bayar da wannan sanarwar ne ta wata takarda wacce ta saki a ranar Laraba ta shugaban ta, Sunday Ashefon, The Punch ta ruwaito.

Yajin Aikin ASUU: Ƙungiyar Daliban Najeriya Ta Yi Barazanar Fara Zanga-Zanga A Ƙasa
Yajin Aikin ASUU: Ƙungiyar Daliban Najeriya Ta Yi Barazanar Fara Zanga-Zanga Daga Ranar 28 Ga Watan Maris. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Ashefon ya ce idan hakan bai tabbata ba daliban Najeriya zasu bi titina suna zanga-zanga.

Kamar yadda takardar ta zo:

“Muna shawartar gwamnatin tarayya da ASUU akan su yi iyakar kokarin su wurin daidaitawa daga yanzu zuwa ranar 28 ga watan Maris na 2022 ko kuma mu dauki namu matakin.
“Muna fatan daga yanzu zuwa ranar 28 ga watan Maris shugabannin ASUU da gwamnati zasu duba illar da wannan lamarin yake da shi ga kasar mu baki daya don su yi gaggawar kawo mafita.
“Ya kamata majalisar tarayya ta yi iyakar kokarin ta wurin ganin ta kawo karshen yajin aikin nan a cikin wannan datsin. Tunda sun hana amfani da dokar da ta hana ma’aikatan gwamnati fitar da yaran su karatu zuwa kasashen ketare, don haka ya kamata su gyara mana makarantun mu don hakan aikin su ne.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai Ya Umurci Duk Masu Riƙe Da Mukaman Siyasa Da Ma'aikatan Gwamnati Masu Son Takara Su Ajiye Aiki

“Idan har yajin aikin nan ya ci gaba, dalibai zasu koma jami’ar da gwamnatin tarayya da ASUU suka samar musu wato ‘Jami’ar titi’, wacce asalin makarantar zata kasance a hanyar tashoshin jirgin sama, dayan reshen kuma a Abuja da sauran wurare da ke titinan jihohi 36 da ke kasar nan.”

Shugaban daliban ya zargi ministan kwadago da ayyuka da na ilimi akan kin samar da mafita ga ASUU

The Punch ta ruwaito yadda ya ci gaba da cewa:

“Don haka ina umartar dalibai da su kawo katifun su da kayan girkin su yayin da sabbin jami’o’in mu zasu fara aiki a Abuja da sauran wurare da ke fadin kasar nan.”

NANS ta koka akan ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige da ministan ilimi, Adamu Adamu akan ci gaba da jagorantar gwamnati wurin sasanci.

A cewarsa, sun gaza wurin samar da matsaya da ASUU.

Dalibai sun koka akan shugabannin ASUU wadanda suka zarga da kin zama da manyan su don sanin asalin matsala da kuma asalin abinda kungiyar take nema wurin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel