An tashi baktatan a makaranta bisa tsoron harin 'yan bindiga a jihar Imo

An tashi baktatan a makaranta bisa tsoron harin 'yan bindiga a jihar Imo

  • Tsoron harin yan bindiga ya tursasa makarantu sallamar dalibai a garin Owerri, babbar birnin jihar Imo
  • An tattaro cewa an rufe makarantun ne sakamakon wata wasika da ke ta yawo a shafukan sadarwa inda aka yi gargadin cewa za a farmaki duk makarantar da ta bude a ranar Litinin
  • Hakazalika hare-haren da yan bindiga suka kai ofishoshin yan sanda a makon da ya gabata ya kara rura wutan tsoro a zukatan mazauna jihar

Imo - Wasu makarantu a birnin Owerri sun tsayar da harkoki cak a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, sannan suka tursasa dalibai komawa gidajensu kan zargin cewa wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba za su kai masu hari.

Kara karanta wannan

Daukar fansa: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa iyaye sun cika da zullumi yayin da suke kwasan yaransu zuwa gida.

An tashi baktatan a makaranta bisa tsoron harin 'yan bindiga a jihar Imo
An tashi baktatan a makaranta bisa tsoron harin 'yan bindiga a jihar Imo Hoto: The Punch
Asali: UGC

Wasu daga cikin shugabannin da ba a bayyana sunayensu ba saboda dalilai na tsaro, sun bayyana cewa dole suka rufe makarantunsu saboda wata wasika da ta yi fice a shafukan soshiyal midiya wacca aka alakanta da yan bindigar da ba a sani ba.

Wasikar ta yi gargadin cewa ba za a kuma yin zirga-zirga ba, sannan za a dunga rufe makarantu a duk ranar Litinin a kasar Inyamurai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsu:

“Za a kai farmaki ga duk makarantar da ta ki bin umurnin.”

Rahoton ya kuma nuna cewa tuni wasu makarantu a hanyar Egbu, Akwakuma, Amakohia, hanyar Owerri-Aba, hanyar Akwakuma, Amakohia, Owerri-Aba suka rufe makarantunsu saboda tsoro.

Lamarin ya kuma shafi wasu makarantu a hanyar MCC/Uratta, hanyar Okigwe zuwa yankin Orji da kuma yankunan bankin duniya.

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Hakazalika, a safiyar yau Litinin, akwai karancin mutane da ababen hawa da ke zirga-zirga a cikin birnin na Owerri.

Wasu daga cikin mazauna birnin da suka yi magana, sun ce hare-haren da aka kai kan ofishoshin yan sanda da gine-ginen mutane ya haifar da tsoro wanda shine ya sa mutane suka yanke shawarar zama a gida.

A cewar wata Tobe Ugwuegbu, mazauniyar Wethedral:

“Hare-hare da suka kai ofishoshin yan sanda daba-daban ciki harda kisan jami’an yan sanda ya dasa tsoro a zukatan mutane inda suke ganin zaman gida na ranar Litinin zai zama mai hatsari.
“Wannan ne dalilin da yasa kuke ganin unguwanni sun zama kamar kufai kowa na zaune a cikin gidajensu. Babu wanda ke so a kashe shi.”

Yan sanda sun kashe yan bindiga 4, sun gano bama-bamai 5 da ba a tayar ba

A wani labarin, mun ji a baya cewa rundunar yan sandan jihar Imo ta kashe yan bindiga biyar da ake zaton yan kungiyar awaren IPOB ne a wani musayar wuta da suka yi a safiyar Lahadi, 20 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Babu ruwana: Babban sakataren gwamnatin Katsina ya karyata cewar yana da hannu a fashi da makami

Lamarin ya faru ne lokacin da yan bindigar suka je kai farmaki ofishin yan sanda da ke karamar hukumar Oru East a jihar Imo.

Kakakin yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Owerri, babbar birnin jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel