APC ba ta Musulmai bane kadai: Gwamna Zulum ya bayyana goyon bayansa ga George Akume

APC ba ta Musulmai bane kadai: Gwamna Zulum ya bayyana goyon bayansa ga George Akume

  • Gwamnan Babagana Zulum ya bayyana goyon bayansa ga tsohon gwamnan jihar Benue, Sanata George AKume matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC
  • Zulum ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a APC su baiwa George Akume goyon baya a zaben da za'ayi ranar 26 ga wata
  • A fahimtar Zulum, inda Akume ya zama Shugaban APC kiristoci zasu ji ana yi da su a harkar jam'iyyar

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari, gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da sauran masu ruwa da tsaki su zabi tsohon gwamnan Benue kuma Ministan harkoki na musamman, Sanat George Akume.

A cewarsa, yana goyon bayan Akume ne saboda adalci da daidaito.

George Akume
APC ba ta Musulmai bane kadai: Gwamna Zulum ya bayyana goyon bayansa ga George Akume
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Kusoshin APC sun yi maza sun ziyarci Sanatan APC ganin PDP sun fara jawo shi kusa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zulum ya bayyana goyon bayansa ne a Abuja lokacin da ya kai ziyara wajen Akume a Abuja.

Yace:

"Wani abu guda da tattare da ni shine bana boye-boye. Ko Shugaban kasa ya san dabi'u na. Domin baiwa Kiristocin jam'iyyar dama damawa da su, Sanata George Akume ya kamata dukkan masu ruwa da tsaki a APC mu goyawa baya."
"Jam'iyyar APC ba ta Musulmi bace kadai. APC jam'iyyar Kiristoci da Musulmai. Saboda haka, dukkan mambobin APC su baiiwa Sanata George Akume baya daman zama Shugaban uwar jam'iyya."

Rikici gabanin taron gangamin APC: Kujerar shugabancin jam'iyya ta raba kan Sanatoci

Batun wanda zai zama shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a majalisa.

Sanatoci uku, Tanko Al-Makura daga Nasarawa, Sani Musa daga Neja da Abdullahi Adamu daga Nasarawa ne suke takarar kujerar.

Kara karanta wannan

Rikici gabanin taron gangamin APC: Kujerar shugabancin jam'iyya ta raba kan Sanatoci

Za a gudanar da babban taron jam'iyyar a ranar 26 ga watan Maris a Abuja, inda za a zabi shugaban jam'iyyar da sauran mambobin kwamitin uwar jam'iyyar.

Daily Trust ta rahoto cewa wani bincike da ta yi ya nuna cewa wasu sanatoci na goyon bayan Abdullahi Adamu saboda ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na goyon bayansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel