Innalillahi: Yara Biyu Sun Mutu Yayin Da Banɗaki Ya Rufta a Jihar Neja

Innalillahi: Yara Biyu Sun Mutu Yayin Da Banɗaki Ya Rufta a Jihar Neja

  • Wasu kananan yara, namiji da mace sun riga mu gidan gaskiya sakamakon gini da ya rufta musu a wata makaranar frimare a Jihar Neja
  • A halin yanzu dai ba a tantance ainihin abin da ya kai kananan yaran kusa da ginin da dama aka ce ya tsufa ba har abin ya faru
  • Wasu majiyoyi sun ce yaran sun tafi wurin suna wasa ne yayin da abin ya faru wasu kuma sun ce sun je neman kayan gwangwan ne

Jihar Niger - An tsinci gawar wasu yara biyu a baraguzan wani bandaki da makarantar frimari ta tunawa da UK Bello, a Paiko, karamar hukumar Paikaro na Jihar Niger, Daily Trust ta rahoto.

A halin yanzu ba a tabbatar da abin da yaran ke yi ba a wurin yayi da ginin da aka ce ya tsufa dama ya rufta musu.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izala ta rabawa yan gudun Hijra da matsalar tsaro ta shafa a Neja kayayayyki

Innalillahi: Yara Biyu Sun Mutu Yayin Da Banɗaki Ya Rufta a Jihar Neja
Yara Biyu Sun Mutu Yayin Da Banɗaki Ya Rufta a Jihar Neja. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wasu majiyoyi sun ce yaran, namiji da mace, suna tallar Pure water ne tare da abokansu a kusa da makarantar a lokacin da ginin ya rufta musu, suka mutu nan take, rahoton Daily Trust.

Wasu sun ce yaran suna roron kayayyakin karafuna ne da za su sayar a kusa da ginin a lokacin da ya rufa.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel