Yanzu-yanzu: Bayan kwana hudu a komar EFCC, an baiwa Obiano beli

Yanzu-yanzu: Bayan kwana hudu a komar EFCC, an baiwa Obiano beli

  • Bayan kwana hudu tsare a hannun hukumar EFCC, an bada belin tsohon gwamnan Anambra Obiano
  • Da alamun karshen gwamnan bata yi kyau yayinda shi da matarsa suka shiga hali mai wuya daga sauka daga mulki
  • Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa har yanzu Willie Obiano bai cika sharrudan belin ba

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, akan beli bayan damkeshi a daren Alhamis, 17 ga wata.

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Litinin a Abuja, rahoton TheNation.

Bawa yace Obiano na basu hadin kai kan binciken da suke gudanawar kansa.

Obiano
Yanzu-yanzu: Bayan hanashi guduwa Amurka, EFCC ta saki Obiano da matarsa Hoto: Anambra State Gov't
Asali: UGC

Bawa yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Sunayen Gwamnoni 33 a Najeriya da hukumar EFCC ta kama bayan tube musu rigar kariya

"Babu siyasa cikin wannan bincike. Kun san EFCC, laifuka muke bincike, muna kama wadanda suka aikata laifi sannan mu kaisu kotu."
"Ana zarginmu da tozarta mutane a kafafen yada labarai. Amma zamu cigaba da bincikenmu yadda ya dace."
"An bashi beli kuma muna jiransa ya cika sharrudan belin, yana bamu hadin kai kuma komai na gudana yadda ya dace."

Awa 10 da sauka daga mulki, EFCC ta damke Willie Obiano yana shirin guduwa Amurka

Hukumar EFCC a dare Alhamis ya damke tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, a tashar jirgin Murtala Muhammad dale Lagos.

EFCC ta damke Obiano ne misalin karfe 8:30 na dare.

An ce yana kokarin guduwa Houston a kasar Amurka ne bayan mika mulki ga sabon Gwamna Charles Soludo.

A watan Nuwamba 2021, hukumar EFCC ta sanya sunan Willie Obiano cikin wadanda take dako.

EFCC ta bukaci hukumar shiga da fice ta sanar da ita duk lokacin da Gwamnan ke kokarin fita daga kasar ta sama ko ta kasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotu ta yanke hukunci kan Bukatar Gwamna Umami da ta tsige kan komawa APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel