Jami’an EFCC sun yi ram da mai gidan coci da FBI ta ke nema ido-rufe saboda damfara

Jami’an EFCC sun yi ram da mai gidan coci da FBI ta ke nema ido-rufe saboda damfara

  • Hukumar EFCC tace ta damke wani mutumin jihar Imo da har jami'an FBI su na bin sahunsa a Duniya
  • Zargin da yake kan Mista Kelechi Vitalis Anozie shi ne ya saci Daloli daga hannun wani Ba Amurke
  • Ragowar abokan barnar wannan mutum da ake nema sun hada da Bright Azubuike da Ekechukwu

Dakarun hukumar EFCC sun yi nasarar cafke wani mutumi wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin sata.

Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na Facebook, Kelechi Vitalis Anozie ya shiga hannunta.

Yanzu haka, Mista Kelechi Vitalis Anozie, yana cikin wanda hukumar FBI ta ke nema a kasashen Duniya.

Federal Bureau of Investigation ce hukumar da ke da alhakin binciken manyan laifuffuka a kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Hushpuppi ya sake tafka satar $400k a Amurka duk da yana hannun FBI

Sanarwar da EFCC ta fitar a shafinta ta tabbatar da cewa an yi ram da Vitalis Anozie ne a makon da ya wuce.

Tun a ranar Alhamis, 10 ga watan Maris 2022 ya fada ragar hukuma bayan an dade ana bin sahunsa.

Jami’an EFCC
Kelechi Vitalis Anozie Hoto: @officialefcc
Asali: Facebook

Zargin da yake kan wuyan Vitalis Anozie sun hada da kutun-kutun, satar kudin mutane da safarar kudi.

Ana tuhumar Anozie da wasu mutane hudu da laifin damfarar wani mutumi da ake kira F.F a kasar waje.

An yi damfarar $18200

F.F yana zaune ne a garin Illinois a Amurka inda wadannan mutane suka damfare shi $135,800 da $47,000.

Idan aka yi lissafi, kudin da ake tunanin wadannan mutane suka sata a hannun F.F ya haura N70, 000, 000.

Kelechi Vitalis Anozie shi ne wanda ya kafa cocin nan na Praying City Church da ke garin Owerri, jihar Imo.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Abokan aikin Kelechi Vitalis Anozie

Sauran wadanda ake zargin sun taimakawa mai cocin wurin aika-aikan su ne Valentine Iro da Ifeanyi Junior.

Sai kuma Bright Azubuike (watau Bright Bauer Azubuike) da kuma Ekechukwu (watau Ogedi Power).

An kama Fasto da wiwi

Kwanaki ne jami’an NDLEA su ka kama Ugochukwu Emmanuel Ekwem dauke da kayan shaye-shaye a filin jirgi.

An cafke Rabaren Ugochukwu Emmanuel Ekwem ne a filin tashin jirgin sama ya na shirin zuwa taro a kasar Kenya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel