Borno: Gobara Ta Yi Ɓarna a Sansanin Ƴan Gudun Hijira, Gidaje 448 Sun Ƙone Ƙurmus

Borno: Gobara Ta Yi Ɓarna a Sansanin Ƴan Gudun Hijira, Gidaje 448 Sun Ƙone Ƙurmus

  • Akalla gidaje 448 na ‘yan gudun hijira suka babbake a makarantar sakandaren gwamnati ta mata da ke karamar hukumar Mafa a Jihar Borno sakamakon wata gobara.
  • Abatcha Ali-Kawu, shugaban karamar hukumar ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis yayin da ya je jajanta wa wadanda lamarin ya shafa
  • Ali-Kawu ya samu rakiyar dan majalisa mai wakiltar Mafa da ke Jihar Borno, Baba Ali-Modu da sauran hamshakai na karamar hukumar

Jihar Borno - Fiye da gidaje 448 na ‘yan gudun hijira a makarantar sakandaren mata ta gwamnati da ke karamar hukumar Mafa a Jihar Borno suka babbake sakamakon wata kazamar gobara.

Shugaban karamar hukumar, Abatcha Ali-Kawu ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis yayin da ya je yin jaje ga wadanda lamarin ya shafa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai Ya Umurci Duk Masu Riƙe Da Mukaman Siyasa Da Ma'aikatan Gwamnati Masu Son Takara Su Ajiye Aiki

Borno: Gobara Ta Yi Ɓarna a Sansanin Ƴan Gudun Hijira, Gidaje 448 Sun Ƙone Ƙurmus
Gobara Ta Yi Ɓarna a Sansanin Ƴan Gudun Hijira a Borno, Gidaje 448 Sun Ƙone Ƙurmus. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Manyan mutane na karamar hukumar ciki har da dan majalisa mai wakiltar Mafa, Baba Ali-Modu suka raka Ali-Kawu zuwa jajen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi asarar miliyoyi

Ya ce gidaje da dama da kayan abinci na miliyoyin nairori sun lalace sanadiyyar gobarar ranar Talata, 15 ga watan Maris.

Shugaban karamar hukumar ya ce wadanda lamarin ya auku da su suna da imani, inda ya ce zai yi aiki da hukumomi don samar musu da mafita.

Malam Ahmadu Abatcha, shugaban ‘yan gudun hijiran, ya ce wutar ta fara ne da misalin karfe 3:40 na rana daga wasu gidajen zuwa wasu.

Abatcha ya ce kokarin mazauna wurin da jami’an tsaro ya taimaka wurin ganin an kawo karshen wutar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel