NNPC: Ganguna fiye da miliyan 100 na danyen fetur sun yi kafa a karkashin Buhari

NNPC: Ganguna fiye da miliyan 100 na danyen fetur sun yi kafa a karkashin Buhari

  • NNPC Limited yana bukatar ya yi karin bayani a kan inda gangunan mai miliyan 109 suka shiga
  • Binciken da ofishin AuGF ta gudanar a 2019 ya nuna shugaban kamfanin yana da aiki a gabansa
  • Sannan akwai alamar tambaya a game da kudin da NNPC suka yi ikirarin sun zuba a assun FAAC

Abuja - Kamfanin NNPC Limited wanda a baya aka sani da hukumar NNPC ta kasa, ta gagara yin bayanin inda ganguna 107,239,436 na danyen mai suka shiga.

Rahoton jaridar The Nation ya bayyana cewa NNPC ba su iya bayanin inda aka kai wadannan gangunan danyen mai da aka ce an yi amfani da su a gida ba.

Akwai yiwuwar an saida wadannan gungunan danyen mai da dararjarsu ta kai N55,891,009,960.63 a lokacin. NNPC ba ta iya yin wani bayani ba.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Jaridar ta fahimci wannan ne a rahoton sakamakon binciken babban mai binciken dukiyar gwamnati.

Binciken da aka yi, ya nuna cewa ba su da bayani a kan yadda aka yi da litoci 22,929.84 na fetur (na N7.06bn) daga manyan tasoshi Ibadan-Ilorin da Aba-Enugu.

Adolphus Aghughu ya aikawa akawun majalisar tarayya sakamakon binciken kudin da suka yi a shekarar 2019. Takardar nan ta isa majalisa ne a watan Agusta.

Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Lissafin FAAC ya saba

Takardar ta kuma tabbatar da an samu sabani tsakanin abin da NNPC ta rika zubawa cikin asusun FAAC da alkaluman da ke gaban babban Akantan gwamnati.

Adolphus Aghughu ya nuna cewa NNPC ta ce ta zuba N1,272,606,864,000 a asusun hadaka na FAAC, amma kuma Akanta Janar ya ce N608,710,292,773.44 ya iya gani.

Kara karanta wannan

Farashin lantarki ya tashi bayan Gwamnati tayi wuf, ta dakatar da tallafin wuta

Hakan na nufin ba a iya yin bayanin inda N663,896,567,227.58 suka shiga ba. AuGF ya bukaci a tambayi shugaban NNPC inda aka kai cikon kudin ko a hukunta shi.

Su wanene a ofis?

Duk wadannan sun faru ne a shekarar 2019, a lokacin da Muhammadu Buhari yake shugaban kasa. Mai girma Buhari ne yake rike da kujerar Ministan mai.

Sai dai ba a nada sababbin Ministoci ba a sa'ilin da abin ya faru a tashoshin man Ibadan-Ilorin da Aba-Enugu ya faru. An yi hakan ne tsakanin Yuni da Yuli.

A daidai Yunin 2019 ne shugaban kasa ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin babban manajan NNPC.

Asara ta hau EFCC

A ranar Larabar nan ne ku ka ji cewa Mr. Wilson Uwujaren ya fitar da jawabi da yawun EFCC yana cewa gobara ta yi masu barna a garin Iriebi a jihar Ribas.

Kakakin na EFCC ya ce Dr. George Ekpungu ya isa wurin da abin ya faru tun a ranar Talata, 15 ga watan Maris da nufin a soma binciken abin da ya jawo wutar.

Kara karanta wannan

Rashin wuta, wahalar mai, ASUU da matsin lamba 6 da ‘Yan Najeriya suka shiga ciki a yau

Asali: Legit.ng

Online view pixel