Babu ruwa na: Ban wanke Abba Kyari ba, cewa nayi a kara yin bincike a kan shi inji Minista

Babu ruwa na: Ban wanke Abba Kyari ba, cewa nayi a kara yin bincike a kan shi inji Minista

  • Abubakar Malami ya ce babu inda ya wanke DCP Abba Kyari daga zargin da suke kan wuyarsa
  • Dr. Umar Jibrilu Gwandu ya fitar da jawabi na musamman, yana bayanin matsayar Malami SAN
  • Ministan shari’an ya bukaci a kara bincike ne a kan Kyari, ya ce bai wanke jami’in ‘dan sandan ba

Abuja - Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ya karyata rade-radin da yake yawo na cewa ya wanke DCP Abba Kyari.

Jaridar Tribune ta rahoto Abubakar Malami SAN yana mai karin haske a kan matsayarsa.

Ministan ya fitar da jawabi ta bakin Mai taimaka masa wajen yada labarai da hulda da jama’a, Dr. Umar Jibrilu Gwandu a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris 2022.

Kara karanta wannan

Hush-Kyari: Ministan shari'a ya yi amai ya lashe, ya wanke Abba Kyari daga zargin damfara

Dr. Umar Gwandu ya ce akwai rashin fahimtar abin da Ministan ya fada a game da binciken da ake yi wa DCP Abba Kyari na hannu a badakalar Hushpuppi.

Gwandu ya ce Matsayar ofishin Ministan shari’a shi ne har yanzu ba a kai ga karshen binciken da ake yi ba a rashin hujjojin da aka samu dangane da rahoton farko.

Hadimin Ministan ya ce AGF ya yi kalamai ne domin a cigaba da gudanar da bincike domin a dauki matakin da ya kamata, ba kokarin wanke jami’in tsaron ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan shari'a
Ministan shari'a, Abubakar Malami SAN Hoto: guardian.ng
Asali: UGC
“Da alamu akwai rashin fahimtar wannan lamarin. Har yanzu bincike ake gudanarwa, don haka ofishin lauyan gwamnati ya bukaci a kara bincike.”

- Dr. Umar Jibrilu Gwandu

This Day ta rahoto Umar Jibrilu Gwandu yana mai cewa makasudin cigaba da binciken shi ne gano gaskiyar wasu abubuwa da har yanzu sun shige duhu.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Rahoton ya ce kawo yanzu, PSC ba ta karbi rahoton binciken da aka gudanar a kan zargin da ake yi wa Kyari da kuma samun shi da laifi da aka yi a Amurka ba.

Ina binciken da IGP ya yi?

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda ba su karbi binciken IGP wanda Marigayi DIG Joseph Egbunike ya gudanar ba inda ya bada shawarar ragewa DCP Kyari matsayi.

Wata majiya tace ana sauraron ’yan sanda har yanzu, bayan an ba su makonni biyu su kammala bincikensu. Sai dai har yanzu ‘yan sanda ba su ce komai ba tukun.

DIG Joseph Egbunike ya mutu

Rahotanni sun bayyana cewa babban jami’in ‘dan sandan kasar nan, Joseph Egbunike ya rasu a makon jiya, makonni kadan bayan ya yi bincike a kan Abba Kyari.

Egbunike shi ne Mataimakin Sufeta-Janar na ‘yan sanda wanda yake kula da bangaren FCID. Marigayin yana cikin 'yan sandan kasar nan masu ilmi da sanin aiki.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan sanda sun mutu yayin da motar tawagar ministocin Buhari ta yi hadari

Asali: Legit.ng

Online view pixel