Yanzun nan: Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis

Yanzun nan: Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis

  • Rahotanni su na bayyana cewa babban jami’in ‘dan sandan kasar nan, Joseph Egbunike ya rasu jiya
  • Joseph Egbunike shi ne Mataimakin Sufeta-Janar na ‘yan sanda wanda yake kula da bangaren FCID
  • Marigayi DIG Egbunike ne jami’in da IGP ya ba alhakin gudanar da bincike a kan DCP Abba Kyari

Abuja - Joseph Egbunike, wanda shi ne Mataimakin Sufeta-Janar mai kula da sashen FCID na rundunar ‘yan sandan Najeriya ya kwanta dama.

Rahoton da ya fito daga Punch a ranar Laraba, 9 ga watan Maris 2022 ya tabbatar da wannan labari.

Kamar yadda mu ka ji, DIG Joseph Egbunike ya fadi ne cikin ofishinsa a yammacin ranar Talata. Tun daga nan bai farfado ba, sai dai aka dauki gawarsa.

Kafin rasuwarsa, Egbunike shi ne 'dan sandan da ya jagoranci kwamitin da IGP Usman Alkali Baba ya kafa domin ya binciki abokin aikinsa, Abba Kyari.

Joseph Egbunike ya gudanar da bincike na musamman a kan zargin da ake yi wa Kyari na hannu wajen safarar makudan kudi da alaka da Ramon Azeez.

Jami’in ‘Dan Sanda
Marigayi DIG Joseph Egbunike Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton binciken da kwamitin Egbunike ya gabatar bai nuna Kyari ya aikata laifin da ake zarginsa da shi karara ba, kuma ba a kai ga aiki da rahoton ba.

Wanene Joseph Egbunike?

Jaridar Pulse ta ce babban jami’in ‘dan sandan mutumin Onistsha ne a jihar Anambra. Marigayin ya na cikin jami’an ‘yan sandan kasar nan masu ilmi.

Marigayi Joseph Egbunikeya yi digirin farko a bangaren Akanta a jami’ar UNN a Nsukka. Sannan yana da digiri na biyu a shari’a da huldatayyar kasashe.

Bugu da kari, DIG Egbunike ya yi digirinsa na uku watau PhD a ilmin laifuffuka a Najeriya.

Ayi hattara - Tsohon AIG

Kwanan nan aka rahoto wani tsohon AIG yana bada shawarar a kara ba Abba Kyari tsaro domin gudun wasu su kashe shi kafin a mikawa kasar Amurka shi.

Ambrose Aisabor yana ganin akwai abubuwa da dama da ‘dan sandan da ake bincike zai iya fallasawa, don haka miyagu za su iya yunkurin hallaka shi.

Binciken Abba Kyari

Kwanaki kun ji cewa ana zargin akwai wadanda suka nemi su wanke DCP Abba Kyari daga zarge-zargen da ake yi masa, har hakan ya raba kan PSC da NPF.

A baya an ji cewa PSC ta na cewa binciken da Joseph Egbunike ya jagoranta a kan DCP Kyari dankare yake da kura-kurai, don haka aka ki karbar rahotonsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel