Da duminsa: Gwamnatin Legas ta dakatar da NURTW daga dukkan tashoshin mota

Da duminsa: Gwamnatin Legas ta dakatar da NURTW daga dukkan tashoshin mota

  • Gwamnatin jihar Legas ta dakatar da dukkan lamurran NURTW daga tashoshi tare da gareji na fadin jihar Legas
  • Hakan ya biyo bayan dakatar da shugaban NURTW na jihar Legas da uwar kungiya ta yi kan zarginsa da rashin da'a
  • Gwamnatin Legas ta kafa kwamiti inda masu ruwa da tsakin kwamitin za su kasance a tashoshi da gareji

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da dakatar da dukkan al'amuran mambobin kungiyar kula da ma'aikatan sufuri, NURTW a jihar.

TheCable ta ruwaito cewa, wannan sanarwan na zuwa ne bayan sa'o'i kadan da kungiyar NURTW reshen jihar Legas ta janye kanta daga kungiyar ta kasa.

Da duminsa: Gwamnatin Legas ta dakatar da NURTW daga dukkan tashoshin mota
Da duminsa: Gwamnatin Legas ta dakatar da NURTW daga dukkan tashoshin mota. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kungiyar NURTW reshen jihar Legas ta janye zamanta mamba a kungiyar ta kasa sakamakon dakatar da Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo kan zarginsa da tsokana, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yakin Ukraine da Rasha: Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea

Kamar yadda takardar da aka fitar a ranar Alhamis ta hannun Gbenga Omotos, kwamishinan yada labarai na jihar Legas, dakatarwan tana daga cikin kokarin gwamnatin na dakile tashin-tashinar da lamarin ya janyo.

"Gwamnatin jihar Legas tana sa ido kan lamurran NURTW. Akwai ikirari da labarai da ke yawo kan shugabancin kungiyar," takardar tace.
“Gwamnatin tana da hakkin tabbatar da kariya ga rayuka da kadarori ta dukkan mazauna Legas da baki. Don haka ta gano cewa akwai bukatar gaggauta dakatar da duk wata hatsaniya ta shugabancin da ke tasowa a NURTW tare da kare 'yan jihar daga makamantan lamurran.
“Bayan duba tanadin doka, gwamnatin ta dakatar da lamurran NURTW, wanda dole ne ta dakatar da su a tashoshin motoci da gareji a dukkan jihar Legas.
"Gwamnatin za ta kafa kwamiti na gaggawa domin ya mamaye tashoshi da gareji. Mambobin kwamitin za su zama masu ruwa da tsaki a harkar.

Kara karanta wannan

DSS ta kama shugabannin kananan hokumomi 2 a Kano kan daukar nauyin dabar siyasa

"Gwamnatin tana kokarin sauke hakkinta na tabbatar da cewa ba a samu tarzoma ba da karya doka a dukkan tashoshi da gareji na jihar Legas."

An ji harbe-harben bindiga yayin da rikici ya barke tsakanin mambobin NURTW

A wani labari na daban, rikici ya barke a unguwar Agbado a karamar hukumar Alimosho a Jihar Legas a ranar Juma'a da safe a yayin da bangarori biyu na kungiyar direbobi ta Najeriya, NURTW, suka kacame da fada a yankin.

Wasu da abin ya faru a gabansu sun tabbatarwa The Punch cewa masu ababen hawa da mutanen da ke wucewa a hanya sun tarwatse don su tsira da rayuwarsu.

An kuma ji harbe-harben bindiga a yayin rikicin da ya faru saboda karbar tikiti a tashohin mota.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel