Lafiyar Sunday Igboho lau: Lauya ya magantu kan belin Igboho bisa uzurin rashin lafiya

Lafiyar Sunday Igboho lau: Lauya ya magantu kan belin Igboho bisa uzurin rashin lafiya

  • Lauyan Sunday Igboho ya bayyana cewa, an yiwa Igboho gwajin lafiya, an gano lafiyarsa lau ba abin da ke damunsa
  • Lauyan ya bayyana haka ne jim kadan bayan rahotanni sun bayyana an saki Sunday Igboho daga magarkama a Benin
  • Lauyan ya bayyana cewa, wasu manyan farfesoshin Yarbawa ne suka yi ruwa suka yi tsaki aka saki Igboho

Ibadan, Oyo - Sunday Igboho, wanda gwamnatin jamhuriyar Benin ta sake daga gidan yari a ranar litinin da ta gabata, ga likitansa, an yi masa gwajin kiwon lafiya an gano lafiyarsa lau, kamar yadda lauyansa, Yomi Alliyu (SAN), ya bayyana a ranar Talata a Ibadan.

Alliyu, ya yi karin haske cewa wasu Farfesoshi biyu, Wale Adeniran da Banji Akintoye ne suka sa aka sako Igboho ba Wole Soyinka ba, kamar yadda ya bayyana a baya a cikin sanarwarsa ta jiya Litinin, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

Lauyan Igobo ya bayyana halin da Sunday Igboho ke ciki
Lafiyar Sunday Igboho lau: Lauya ya magantu kan belin Igboho bisa rashin lafiya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Mista Alliyu ya ce Likitocin Igboho sun bayyana cewa ba abin da ke damunsa, kuma lafiyarsa kalau.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Daya daga cikin sharuddan sakinsa shi ne ya ci gaba da zama a jamhuriyar Benin a halin yanzu cikin cikakken tsaro. Hakazalika lafiyarsa lau.
"Za mu ci gaba da jinjina gudunmawar da Farfesa Wale Adeniran ya bayar saboda rawar da ya taka wajen shawo kai da sakin wanda muke karewa."

Alliyu a ranar Litinin din da ta gabata ya ce an saki Igboho bisa yarjejeniyar cewa ba zai bar cibiyar lafiya ko Cotonou ba ko da kuwa meye dalili.

Kungiyar Yarbawa ta sa baki, Jamhuriyar Benin ta saki dan awaren Yarbawa Sunday Igboho

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta saki dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Ighoho bayan doguwar tsarewa da ya sha.

Kara karanta wannan

Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari bisa umarnin wani gwamna

Hadin kan Yarbawa a kungiyoyin rajin kare hakkin Yarabawa ta Ilana Omo Oodua Worldwide ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Sanarwar wadda mai magana da yawun Ilana Omo Oodua, Mista Maxwell Adeleye, ya fitar, mai taken, ‘Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta Saki Dan rajin kare al’ummar Yarabawa, Sunday Adeyemo Ighoho ga shugaban Yarbawa, Banji Akintoye; Masanin harshen Faransanci, Adeniran'.

Har yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai game da sakin Sunday Igboho da ke tsare a Jamhuriyar Benin tun shekarar 2021.

Ba dani ba: Lauyan Sunday Igboho ya zare hannunsa a rikicinsu da gwamnatin Buhari

A wani labarin, Lauya Pelumi Olajengbesi, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Sunday Adeyemo, shugaban 'yan awaren Yarbawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi murabus daga tawagar kare dan awaren.

Idan baku manta ba, a baya mun kawo muku rahotannin yadda gwamnatin jamhuriyar Benin ta kame Sunday Igboho ta tasa keyarsa magarkama a kasar.

Kara karanta wannan

Kungiyar Yarbawa ta sa baki, Jamhuriyar Benin ta saki dan awaren Yarbawa Sunday Igboho

Daga nan ne batutuwa suka fara girma, gwamnatin Najeriya ta fara bibiyar yadda za ta dawo dashi Najeriya don gurfanar dashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.