Yan bindige sun kashe mutum 5, sun kona Tanka makare da man fetur a hanyar Birnin Gwari-Kaduna

Yan bindige sun kashe mutum 5, sun kona Tanka makare da man fetur a hanyar Birnin Gwari-Kaduna

  • Yan bindiga sun sake kai hari kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, sun kashe mutum 5 sun jikkata wasu
  • Wani ɗan yankin ya shaida cewa yan ta'addan sun kona wata Tankar dakon mai Kurmus, wacce ta ɗakko litar mai 33,000
  • Ya yi kira ga shugaban ƙasa Buhari ya umarci sojoji sun yi kaca-kaca da yan ta'addan a maboyarsu dake yankin

Kaduna - Yan ta'adda sun halaka mutum 5 a ƙauyen Manini, kusa da Kuriga dake kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Maharan sun kuma ƙona wata Tankar dakon Man fetur ƙurmus mai ɗauke da lita 33,000 a kan hanyarta ta zuwa Birnin Gwari.

Shugaban wata kungiyar tsaro da kawo cigaba a Birnin Gwari, Alhaji Ibrahim Abubakar Nagwari, shi ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

2023: Ina kwadayin zama shugaban ƙasa ne saboda muhimmin abu daya, Tinubu

Yan bindiga
Yan bindige sun kashe mutum 5, sun kona Tanka makare da man fetur a hanyar Birnin Gwari-Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana sunayen waɗan da aka kashe da suka haɗa da, Saifudeen Lawal Isa, da kuma wani ɗan asalin garin Birnin Gwari.

Ya ce mutum ɗaya daga Kuriga, biyu daga Udawa na daga cikin mutanen da yan ta'adda suka kashe yayin harin.

Alhaji Nagwari ya ce:

"Lamarin mara daɗi ya auku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma lokacin da yan ta'addan suka buɗe wa matafiya wuta a lokuta uku. Mutum biyu mata da wasu biyar suka jikkata."
"Yan ta'addan sun kona Tanka ƙurmus mai ɗauke da Litan man fetur 33,000 zuwa Birnin Gwarai a dai-dai kauyen Minini."
"Hari da kuma kashe mutane a kan hanyar ya saba faruwa kullum. Lamarin ya ƙara dagula jeka-ka-dawon motoci a kan hanyar Birnin Gwari-Kaduna."

Muna bukatar Buhari ya sa baki

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sojojin Rasha sun zagaye birnin da Daliban Najeriya ke ciki a Ukraine ba hanyar fita

Mutumin ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, cikin gaggawa ya kaddamar da yaƙi kan yan ta'addan da kuma tada maboyarsu da bama-bamai.

Har zuwa yanzun, babu wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin Kaduna ko hukumar yan sanda kan wannan harin na baya, kamar yadda Punch ta rahoto.

A wani labarin kuma Mata ta kai karar Mijinta Kotu kan yana cusa mata tissue a Al'aura idan suna saduwa

Wata mata ta maka Mijinta Uban ƴaƴanta a gaban Kotu bisa zargin yana cusa mata tarkace a al'aura yayin saduwar aure.

Matar ta shaida wa alkalin Kotun a Abuja cewa ta ɗana masa tarko ta tabbatar da abin da yake mata, amma mijin ya musanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel