An yi sauyi a kamfanin simintin Dangote, Halima Dangote ta maye gurbin Sani Dangote

An yi sauyi a kamfanin simintin Dangote, Halima Dangote ta maye gurbin Sani Dangote

  • Kwanan nan ne kamfanin nan na Dangote Cement Plc ya bada sanarwar nada sabuwar babbar darekta
  • Halima Aliko Dangote ta dare kujerar Non-Executive Director daga ranar 26 ga watan Fubrairu 2022
  • Bisa dukkan alamu, Halima Aliko-Dangote ce ta dare kujerar da Marigayi Alhaji Sani Dangote ya bari

Lagos - Ms Halima Aliko-Dangote za ta rike mukamin babbar darekta maras iko a kamfanin simintin Dangote. Nairamterics ta fitar da wannan rahoto.

A wata sanarwa da Dangote Cement Plc ta fitar kwanan nan, an ji cewa Halima Aliko-Dangote ta fara rike wannan matsayi daga 26 ga watan Fubrairun 2022.

Sakataren kamfanin simintin, Edward Imoedemhe ya fitar da wannan sanarwa a wata takarda.

Hakan na zuwa ne bayan Halima Aliko-Dangote ta shafe tsawon shekaru 13 ta na rike da manya mukamai. Halima ‘diya ce a wurin Alhaji Aliko Dangote.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Naɗa Ɗangote, Ɗantata Da AbdusSamad Muƙami a Hukumar Zakka

Kujerar Sani Dangote

Jaridar Premium Times ta ce Halima Aliko-Dangote za ta maye gurbin da baffanta, Marigayi Sani Dangote ya bari. Darektan kamfanin ya rasu a karshen 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin rasuwarsa, Sani Dangote shi ne mataimakin kamfanin Dangote Group, kuma yana cikin darektocin kamfanin simintin ‘danuwansa, Aliko Dangote.

Halima Dangote
Halima tare da su Bill Gates da Aliko Dangote Hoto: www.forbes.com
Asali: UGC

Wacece Halima Aliko-Dangote?

Ms. Halima Aliko-Dangote ita ce babbar darekta mai iko watau GED na sashen harkokin kasuwanci na kamfanin Dangote Industries Limited (DIL).

Wannan kamfani da takwarorinsa sun kware wajen harkokin sukari, gishiri, siminti da kuma mai.

Kafin yanzu ‘diyar Aliko Dangote tayi aiki a matsayin darekta a kamfanin Dangote Flour Mills. Sannan ta taba rike darekta a NASCON Allied Industries Plc.

Rahoton ya ce yanzu haka Halima Aliko-Dangote ce shugabar majalisar da ke sa ido a kamfanin The Africa Center (TAC) a Amurka, kuma ta na cikin WCD.

Kara karanta wannan

Abin da PDP za tayi kafin tayi nasara a zabe - Gwamna Tambuwal ya bada lakanin 2023

Ribar kamfanin Dangote

A ranar Litinin ne kamfanin ya bada sanarwar makukun ribar da ya samu a shekarar nan ta 2021. Abin da kamfanin simintin ya samu a yanzu ya haura N1.4tr.

A baya kun ji cewa kamfanin Dangote Cement Plc ya samu kazamar riba daga watan Junairu zuwa Satumban 2021. Michel Puchercos ya bayyana wannan.

A cikin watanni tara, kamfanin simintin ya samu Naira Tiriliyan 1.02 da ribar Naira biliyan 450.5.

Asali: Legit.ng

Online view pixel