Bikin 13: Gwamna Zulum ya aike da sakon farin ciki ga Mai Martaba Shehun Borno

Bikin 13: Gwamna Zulum ya aike da sakon farin ciki ga Mai Martaba Shehun Borno

  • Gwamnan jihar Borno ya taya Mai Martaba Shehun Borno murnar cika shekara 13 da hawa kan karagar mulkin Sarauta
  • Zulum ya ce duk wani haifaffen jihar Borno yana alfahari da Masarautar Shehu, kuma tawali'unsa ya sa ba'a wani shagali a bikin
  • A madadin gwamnatin Borno da mutanen jihar, Zulum ya yi wa Basaraken fatan Alheri da addu'ar karin lafiya

Borno - Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya bayyana mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi, da jagora nagari, wanda ke tsayawa mutanensa komai rintsi.

Gwamna Zulum ya yi wannan furucin ne yayin da Basaraken ke bikin cika shekara 13 a kan karagar mulki.

A wata sanarwa da aka sa a Facebook ɗauke da sa hannun kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, Zulum ya ce mutuntaka da kyawun halin Shehun Borno ya sa bikin kara shekara a kan mulki ba ya karaɗe kasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya daba wa dan Acaba makami har lahira kan ya buge masa Kare a Gombe

Shehun Borno da Zulum
Bikin 13: Gwamna Zulum ya aike da sakon farin ciki ga Mai Martaba Shehun Borno Hoto: The Governor of Borno State/Facebook
Asali: Facebook

A kalamansa gwamnan ya ce:

"Bisa alfahari da jin daɗi, Ni a madadin gwamnatin Borno da al'ummar jiha baki ɗaya, muna taya Uban mu, mai martaba Shehun Borno murnar cika shekara 13 a karagar mulki, tun bayan naɗa shi a 2009."
"Na jima ina nazarin cewa bikin kara shekara kan Mulki na mai martaba Shehun Borno ba'a wani shagali sosai idan ka kwatanta da sauran masarauntun dake faɗin kasar nan."

Meyasa ba'a shagali sosai a Masarautar Shehun Borno?

Gwamna Zulum ya ƙara da cewa a fahimtarsa, tawali'u da kankan da kai na Shehun Borno ya sa ba a shirya wani shagali da zai jawo hankalin duniya.

"A tunani na, haka na faruwa ne saboda tawali'un Shehu. Ina tunanin ya kamata mu yi murna, sabida ba kamar mu bane da muke da wa'adi a Ofis. Ofishin Shehu na dindindin ne a Borno.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

"Duk wani ɗa da ɗiya mace suna alfahari da tambarin Sarautar Shehun Borno. Kamar yadda muka saba duk shekara muna tura sakon fatan Alheri domin murnar kara shekara ga muhimman mutane."
"Zamu yi abin da ya fi haka domin taya Uban mu murna, dadin daɗawa Shehu ya kawo lokacin da muke fuskantar kalubale, duk da haka ya tsaya wa mutanensa cikin daɗi da rashin daɗi."

Zulum ya yi addu'a ga mai martaba Shehun Borno da cewa Allah ya kara masa karfin guiwa da lafiya domin cigaba da jagorancin al'umma.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya amince da dala miliyan $8.5m na kwaso yan Najeriya daga Ukraine

Karamin minista a ma'aikatar harkokin waje, Zubairu Dada, ne ya faɗi haka jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa a Abuja.

Ya ce jirage uku da zasu yi aikin zasu bar Najeriya zuwa kasashe huɗu dake makwaftaka da Ukraine

Asali: Legit.ng

Online view pixel