'Akwai Matsala' CAN ta bayyana babban abin da take tsoron ka iya faruwa a zaben 2023

'Akwai Matsala' CAN ta bayyana babban abin da take tsoron ka iya faruwa a zaben 2023

  • Ƙungiyar kiristoci ta ƙasa (CAN) ta bayyana babban barazanar da ka iya faruwa da zaɓen 2023 dake tafe
  • A cewar ƙungiyar addinin a Najeriya, matsalar tsaron da ake fama da ita ka iya shafar gudanar da babban zaɓen
  • Shugaban CAN na ƙasa, Dr Samson Ayokunle, ne ya faɗi haka yayin da shugabannin kiristoci suka gana da wakilan EU

Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bayyana cewa zaben 2023 da ake ta shirye-shirye da zumuɗin zuwansa ka iya zama mara inganci.

Kungiyar ta ce matsalar tsaro da yan ta'adda, yan bindiga da masu garkuwa suka jefa Najeriya shi ne, "babban barazana" ga zaben 2023, kamar yadda Punch ta rahoto.

Sanarwan da kungiyar ta fitar ranar Laraba, 2 ga watan Maris, 2022, ta nuna cewa shugaban CAN, Dakta Samson Ayokunle, ya yi wannan furucin ne yayin gana wa da wakilan kungiyar tarayyar turai (EU).

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shahararren ɗan Fafutuka ya bayyana kudirinsa na gaje Buhari a 2023

Shugaban ƙungiyar CAN, Dakta Ayokunle
'Akwai Matsala' CAN ta bayyana babban abin da take tsoron ka iya faruwa a zaben 2023 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ayokunle, wanda yana ɗaya daga cikin shugabannin majalisar haɗin kan addinai, ya ce yanayin tsaro ka iya shafar sahihanci da ingancin zaben dake tafe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan ya yi bayanin cewa matsalar da ƙasa ke ciki game da tsaro ba zata bar mutane su fita runfunan zaɓe ba, saboda tsoron garkuwa, cutarwa ko kisa.

A cewar shugaban CAN, "Alamu sun nuna gwamnati na faɗi tashin daƙile yanayin mara kyau, kokarin da suke a yanzu bai kai ya kawo ba."

Bisa haka, Ayokunle ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su tashi tsaye su kawo ƙarshen yaɗuwar matsalar tsaro a Najeriya.

A kalamansa ya ce:

"Idan haka ta cigaba da faruwa, masu kaɗa kuri'u da yawa ba zasu fito ba, saboda haka sakamakon zaɓen ba zai zama gamsasshe ba."

Bai dace INEC ta shiga siyasa ba - Shugaban CAN

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Gwamnatin Buhari zata fara jigilar dawo da yan Najeriya da yaƙin Rasha-Ukraine ya rutsa da su

Rabaran Ayokunle ya yi kira ga hukumar zaɓe INEC kada ta tsoma kanta cikin harkokin siyasa yayin gudanar da aikin dake kanta.

Ya kuma bukaci mambobin hukumar INEC da suke yan amshin shatan jam'iyya mai mulki su gaggauta yin murabus ko a fatattake su domin gudun yin magudi.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun halaka mutanen da ba'a san yawansu ba

Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun aikata mummunar ɓarna a kauyen Amangwu Ohafia dake yankin jihar Abia.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun halaka mutane ma su adaɗi mai yawa, wanda har yanzun ba'a gano yawan su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel