Pure Water: Kungiyar Masu Sana’ar Ruwar Leda Sunyi Ƙarin Kuɗi

Pure Water: Kungiyar Masu Sana’ar Ruwar Leda Sunyi Ƙarin Kuɗi

  • Kungiyar masu sarrafa ruwan leda wanda aka fi sani da fiyo wota, ATWAP sun sanar da batun karin farashin ko wacce jaka, daga N150 zuwa N200
  • Shugaban kungiyar na yankin Oye-Ekiti da Ikole-Ekiti, Tale Oguntoyinbo ya sanar da hakan ta wata takarda a Oye-Ekiti ranar Juma’a inda ya sanar da dalilan tashin farashin
  • A cewar Oguntoyinbo, karin farashin ya biyo bayan yadda farashin kayan aiki ya karu, kuma wajibi ne hakan don samar da ingantaccen ruwa ga kwastomomi

Ekiti - Kungiyar masu sarrafa ruwan leda wanda aka fi sani da fiyo wota sun bayyana batun tashin farashin jakar ruwan daga N150 zuwa N200 saboda tashin farashin kayan aiki, Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaban kungiyar na yankin Oye-Ekiti da Ikole-Ekiti, Tale Oguntoyinbo ya sanar da hakan ta wata takarda wacce ya saki a Oye-Ekiti ranar Juma’a.

Masu sarrafa fiyo wota sun sanar da batun karin farashin ruwan
Masu sarrafa 'Pure Water' sun sanar da batun karin farashin ruwan. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

A cewar Oguntoyinbo ya tashin farashin kayan aiki ne ya janyo aka tayar da farshin ruwan don samar da ingantaccen ruwa ga kwastomomi.

A cewarsa:

“Ruwa yana da muhimmanci a rayuwar kowa, ruwa shi ne jigo, don haka akwai bukatar a samu kudin gyara da sarrafa ruwan a ko yaushe.
“Don samar da ruwa mai inganci da kuma tabbatar da ruwan ya shawu, hakan yasa wajibi ne tayar da farashin daga N150 zuwa N200.”

Rashin tallafi daga gwamnati ma ya taka babbar rawa wurin tashin farashin

Shugaban kungiyar kamar yadda Daily Nigerian ta nuna ya ce duk da hakan ba abu mai sauki bane ga jama’a kuma gwamnati bata tallafa wa masu sarrafa ruwan, hakan yasa sai an kara farashin.

A cewarsa, a garuruwa da dama, leda da wasu abubuwan da ake amfani da su wurin sarrafa ruwan har da wutar lantarki sun tashi sun koma tsakanin N200 da N250.

Oguntoyinbo ya koka akan yadda gwamnatin jihar ta kasa gyara akan halin da ma’aikatu da dama suke ko kuma su siya musu ababen hawa don kai kaya daga wuri zuwa wuri.

Ya bai wa kwastomomi hakuri inda yace halin da Najeriya take ciki su ne suka janyo tashin farashin, inda ya yi fatan Ubangiji ya saukaka.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel