Hukumar NDLEA ta gano gonakin tabar wiwi masu girman hekta 255, ta kone su kurmus

Hukumar NDLEA ta gano gonakin tabar wiwi masu girman hekta 255, ta kone su kurmus

  • Jami'an hukumar NDLEA sun yi babban aiki, sun kama wasu miyagun kayayyaki a jihar Ondo da ke Kudu maso Yamma
  • An kama tare da konawa da lalata gonakin tabar wiwi a wasu kananan hukumomi biyar na jihar ta Ondo
  • Shugaban hukumar NDLEA ya magantu, ya yabawa jami'ansa bisa kyakkyawan aikinsu tare da kara musu karfin gwiwa

Jihar Ondo - Daily Trust ta rahoto cewa, jami’an hukumar NDLEA a wani gagarumin samame da suka kwashe kwanaki bakwai suna yi sun lalata wasu gonakin tabar wiwi masu girman hekta 255 da suka wanzu a kananan hukumomi biyar na jihar Ondo.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya bayyana haka a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an kama mutane 13 da ake zargi da 250kg na irin tabar wiwi da kuma 63.85kg na tabar wiwi a yayin samamen da aka yi cikin dazukan.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

Yadda aka kone gonakin tabar wiwi
Rundunar NDLEA ta gano gonar tabar wiwi mai girman hekta 255, ta kone ta kurmus | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana dazuzzukan kamar haka; Omolowo/Powerline, Ipele, Ala, Ogbese, Utte da Okuluse wadanda suka wanzu a kananan hukumomi biyar na jihar.

Kayayyakin da aka kama, aka lalata kana aka kone su

A cewarsa:

“Aikin mai suna ‘Operation Abub’, wanda aka fara a dajin Ogbese a ranar Talata 15 ga Fabrairu an ci gaba da yinsa har zuwa ranar Litinin 21 ga Fabrairu 2022.
“A dajin Ogbese, an kama wani da ake zargi, Olatunde Olaoluwa a gonarsa ta tabar wiwi mai girman hekta 10, wadda aka lalata da kuma kone ta tare da wasu gonakin tabar wiwi da suka bazu a gabar kogin Ogbese.
“Washegari, 16 ga watan Fabrairu, jami’an hukumar da yawansu sun kai farmaki dajin Ipele inda suka kama Amos Mark, Luke Job, Monday Momoh, da Otunuya Waya inda aka lalata gonar noman rani ta tabar wiwi mai girman hekta 19.”

Kara karanta wannan

Kusoshin Gwamnati za su amsa tambayoyi a Majalisa kan zargin cuwa-cuwar albashi

Ya kuma ce daya daga cikin wadanda ake zargin da ya tsere a lokacin da aka kone gonakin, an kama shi a gidansa.

A ranar Laraba 17 ga watan Fabrairu ne al’ummar Omolowo da ke yankin Ogbese suka kama wata Mary Udonije a wata gona mai fadin hekta 10 dauke da irin tabar wiwi 16.5kg da kuma tulin tabar wiwi mai nauyin 4.5kg.

Haka kuma an kwato injuna da fanfunan ban ruwa na noman rani mai tiyo din da tsawonsa ya kai sama da mita 700 don shayar da haramtacciyar shukar.

Har ila yau, an kuma kama irin wiwi da bai yi kasa da 154kg ba a dajin Ala da ke karamar hukumar Akure ta Arewa tare da lalata gonakin noman tabar na rani mai girman sama da hekta 30 tare da kone su.

An kama wani da ake zargi, John Mike wanda ya yi ikirarin cewa shi lebura ne da irin tabar wiwi 2.5kg, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jami'an yan sanda sun damke jami'in Soja da tabar Wiwi a Bauchi

Sauran ayyuka a ranakun da aka yi aikin

A rana ta hudu na aikin, an lalata gonar tabar wiwi mai girman hekta 54 a dajin Utte da Okuluse da ke karamar hukumar Ose ta jihar.

Haka kuma a gonar an kwato irin tabar wiwi mai nauyin 95kg, 2.5kg na tabar wiwi da aka sarrafa da kuma injin fanfo mai dogon tiyo.

A rana ta biyar, an kama wani Anthony Agbe, mai shekaru 58, tare da 43kg na tabar wiwi a cikin wata gona da aka lalata a Ogbese.

Ya yi ikirarin cewa wani Henry Daniel, (da aka fi sani Calendar) ne ya ba shi kwangilar wanda yanzu ake nema don taimakawa wajen tattara tabar wiwin din da aka lalata.

An kama wani Ahmadu Abubakar tare da bindigogi uku a cikin wata bukka da ke cikin wata gona inda aka lalata sama da hekta uku a karamar hukumar Akure ta jihar.

Kara karanta wannan

Karfin hali: EFCC ta kwamushe wani mutum da ke ikirarin shi PA ne na gwamnan jiha

A ranar karshe ta aikin, an lalata sama da tuli 50 na tabar wiwi da suka bazu a hekta 47 tare da kama 2kg na irin tabar wiwi.

Hakazalika, an kama wani mai suna Olorunlogo Lekan a cikin wata babbar gona ta wiwi mai girman hekta 10 a dajin Ala Dajin kafin jami'an NDLEA na jihohin Edo, Oyo, Osun, Ekiti da Ondo su kone ta.

An kuma lalata tare da kone akalla hekta 72 na sauran gonakin tabar wiwi da ke kusa da yankunan da aka runtuma wannan aikin.

Shugaban Hukumar NDLEA, Mohamed Buba Marwa, ya yabawa hafsoshi da jami’an hukumar bisa wannan namijin aiki.

Ya kuma umarce su da su nemo karin irin wadannan gonaki a kowane bangare na kasar domin daukar matakin gaggawa akansu.

Babbar magana: Bugagge ya zuba omo a ledar ruwan maganin majinyaci, ya gamu da fushin alkali

A wani labarin, an yanke wa wani mutum dan shekaru 32 hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa laifin zuba ruwan omo a ledar ruwan maganin wani majiyyaci yayin da yake kwance a asibiti don jinyar kuna.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NDLEA ta cafke Mutumin Indiya da aka samu da kwalaben codeine 134,000

Majiyoyi sun bayyana a ranar Talata cewa mutumin ya aikata laifin ne a wani asibiti da ke Daejeon, mai tazarar kilomita 160 Kudu da birnin Seoul, a watan Maris din shekarar 2021.

Bayan saka sinadarin, majiyyacin ya koka da jin ciwon kirji wanda ya kai ga wata ma'aikaciyar jinya ta canza ruwan ledan, amma mutumin ya sake zuba ruwan omon a bayan sa'a daya, in ji majiyoyin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel