Jami'an yan sanda sun damke jami'in Soja da tabar Wiwi a Bauchi

Jami'an yan sanda sun damke jami'in Soja da tabar Wiwi a Bauchi

  • Kwanan guda bayan damke Abba Kyari da laifin safarar waya, yan sanda sun damke Soja da tabar wiwi
  • Sojan ya bayyana cewa bai da masaniyar yana dauke da tabar a cikin motarsa
  • Hukumar yan sanda tace zata gudanar da bincike kansa sannan ta mikashi da hukumar NDLEA

Bauchi - An damke wani jami'in Soja dauke da nadin tabar wiwi guda 81 ranar Talata a jihar Bauchi yayinda yan sanda masu sintiri suka tsayar da motoci a kan titi.

Kwamishanan yan sandan jihar, Umar Sanda, ya bayyana cewa jami'ansa sun tare mota kirar Toyota Highlander da wani Soja masi suna Yusuf Gongpolai Adams ke tukawa.

Jami'an yan sanda sun damke jami'in Soja da tabar Wiwi a Bauchi
Jami'an yan sanda sun damke jami'in Soja da tabar Wiwi a Bauchi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da kakakin yan sandan jihar ya saki, kwamishanan yace Soja na aiki ne a 145 Batallion dake Abia amma ya zo karatu makarantar fasahar Soji dake jihar Benue, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Yadda muka lallasa APC a zaben Abuja, haka zamuyi mata a 2023: PDP

Yace:

"A ranar 06/02/2022 kimanin karfe 12 na rana, jami'an sintiri a hanyar Bauchi-Darazo sun damke wata mota Toyota Highlander da wani Yusuf Gonpolai Adams ke tukawa."
"Ya ce shi Soja ne tare da 145 Battalion, Abia."
"Yayin bincike ya amince da aikata laifi. Daga cikin abubuwan da aka samu a hannunsa akwai nadin ganye guda 81 wanda ake zargin wiwi ne, rigar Soja 1, tayoyin biyu, .... da wasu layu."
"Ana cigaba da bincike kuma za'a mikashi ga hukumar NDLEA."

Amma, Sojan ya bayyana cewa bai da masaniyar yana dauke da tabar a cikin motar.

Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA

A wani labarin kuwa, Hukumar hana amfani da miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta yi martani da jawabin Sifeto Janar na yan sanda inda yayi kira ga a hukunta jami'an hukumar da suke taimakawa wajen shigo da hodar Iblis Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa

Daily Trust ta ruwaito kakakin hukumar, Femi Babafemi, da cewa hukumar ba zata yi wani rufa-rufa ba, ko wanene sai an tona masa asiri.

Yayinda aka tambayesa shin me yasa ba'a ambaci sunayen jami'an NDLEA da sukayi safarar tare da Abba Kyari ba, Babafemi yace hukumar ba zata boye kowa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel