Ka da Buhari ya fita ofis, za mu kashe titunan Abuja sai ASUU ta dawo aiki inji Kungiyar Dalibai
- Kungiyar daliban Najeriya ta ce za ta rufe duk hanyoyin da za a bi a iya shiga birnin tarayya Abuja
- NANS za ta yi wannan ne domin nuna rashin jin dadinta kan yajin-aikin da ASUU ta sake tafiya
- Yazid Tanko Muhammad ya ce za su yi zanga-zanga a kwaryar birnin Abuja domin farfado da ilmi
Abuja - Kungiyar NANS ta daliban Najeriya ta na barazanar toshe duk wasu hanyoyin da suke shiga garin Abuja idan ASUU ba ta janye yajin-aikinta ba.
Daily Trust ta rahoto NANS tana mai cewa za ta cika titunan birnin Abuja da zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin matakin da kungiyar ASUU ta dauka.
Mataimakin shugaban kungiyar daliban kasar, Yazid Tanko Muhammad, ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da manema labarai a safiyar ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Kungiyar ASUU za ta yi zaman farko da Gwamnatin Tarayya mako 1 da fara yin yajin-aiki
Yazid Tanko Muhammad ya ce hakan ya zama dole domin ceto harkar ilmi daga yawan yajin-aiki.
“Abin da ya sa muka zabi mu yi zanga-zanga shi ne, shi kadai ne yaren da za a iya fahimta, shiyasa za mu nunawa Duniya yadda muka ji game da yajin-aikin.”
“Saboda haka zanga-zanga ce da idan mu ka fara, ba za mu daina ba har sai an shawo kan lamarin, malaman jami’a sun koma bakin aiki.” – Yazid Mohammed.

Source: UGC
Buhari ya zauna a gida - Yazid Tanko Muhammad
Yazid Tanko Muhammad ya ba Mai girma Muhammadu Buhari shawarar ya yafe zuwa ofis a ranar.
“Za mu rufe duka hanyoyin shiga Abuja daga jihohin Kogi, Kaduna da kuma Nasarawa. Hakan na nufin za a toshe gaba daya birnin Abuja a wannan ranar.”
“Za kuma mu rufe sakatariyar tarayya. Shiyasa mu ke kira ga shugaban kasa da ya goyi-bayanmu, ta hanyar rashin fitowa zuwa aiki a irin wannan ranar.”

Kara karanta wannan
Rashin tsaro: Tsohon Shugaba Jonathan ya yi hasashen yadda zaben 2023 zai kasance
“Buhari ya yi hakuri ya zauna a gida tun da kowa dalibi ne; ko Minista, Sanata, ‘Dan Majalisa ne, duk sun taba zama dalibai kafin su kai wannan matsayin yau.”
- - Yazid Tanko Muhammad
Sahara Reporters ta rahoto cewa shugabannin ASUU na kasa, Asefon Sunday da Adekitan Lukman sun yi alkawari za su tare tituna idan ba a dawo aiki ba.
Majalisa ta sa baki
Dazu da safe ne mu ka ji cewa Majalisar wakilai ta tabo maganar yajin-aikin da ake yi a jami’o’i a zaman farkon da tayi a makon nan, ta ce ya kamata a koma karatu.
Honarabul Dozie Nwankwo ya koka a game da yadda malaman jami’o’i suke shiga yajin-aiki bini-bini. 'Dan majalisar na Anambra ya na ganin dole a cika ka'idar MoU.
Asali: Legit.ng