Harkar kwaya: Abba Kyari zai iya karasa rayuwarsa ta Duniya a kurkuku a dokar NDLEA

Harkar kwaya: Abba Kyari zai iya karasa rayuwarsa ta Duniya a kurkuku a dokar NDLEA

  • Dokar hukumar NDLEA tayi tanadi ga duk wanda aka samu da irin laifin da ake zargin Abba Kyari
  • Muddin Abba Kyari ya aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa, zai iya karasa rayuwarsa a kurkuku
  • Baya ga hukuncin daurin rai da ke jiran mai wannan laifi, wanda ake tuhuma zai iya rasa dukiyarsa

Wani rahoto da jaridar Punch ta fitar a ranar Alhamis ya nuna Alkali zai iya yankewa wanda aka samu da wannan laifi, hukuncin daurin rai a gidan yari.

A lamarin Abba Kyari, jim kadan bayan hukumar NDLEA ta bada sanarwar cewa tana nemansa, sai aka ji jami’an ‘yan sanda sun bada sanarwar cafke shi.

Mai magana da yawun bakin dakarun ‘yan sanda na kasa, Muyiwa Adejobiya ya shaidawa Duniya cewa sun mika DCP Abba Kyari ga hukumar NDLEA.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Rundunar ‘yan sandan ta kuma fito fili ta zargi Abba Kyari da cewa an ga yana karbar makudan Daloli a hoto, wanda yin hakan ya sabawa aikin jami’in tsaro.

Zargin da ke wuyan Abba Kyari

Hada-kai wajen laifi

Hukumar NDLEA ta na zargin Abba Kyari da hannu wajen harkar safarar miyagun kwayoyi da ake yi na kasa da kasa tsakanin Brazil-Habasha-Najeriya.

Harkar kwayoyi

Ana tuhumar Kyari da wasu jami’ai hudu da hannu wajen harka da kilogram 25 na hodar iblis. Rahotanni sun bayyana cewa an dakatar da jami'an daga aiki.

NDLEA
Jami'an NDLEA Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Taba kwayoyi/hujjoji

Wani zargin da NDLEA take yi wa ‘dan sandan shi ne, shi da jami’ansa sun nemi su yi gaba da kilo 15 na hodar iblis da aka karbe, sai su bar kilo 10.

Kara karanta wannan

Harkallar kwaya: Abba Kyari ya yi fallasa, NDLEA ta je kotu neman ci gaba da tsare shi

Hukumar yaki da kwayar ta ce Kyari ya yi niyyar maye gurbin kwayar da zai dauka da na bogi. A haka ya shirya sulalewa da kwayar, sai ya saida.

Baya ga zargin sata, hakan zai zama ‘dan sandan ya kai hannunsa ga abin da zai zama hujja a kotu. Aikata wannan a karonkasa babban laifi ne.

Safara da saida hodar iblis

A cewar kakakin hukumar NDLEA, Kyari ya dauki kilo 15 na kwayan, ya rabawa wasu; ya ba su kilo 7, sannan shi da wasu yaransa su ka saida kilo 8.

Bugu da kari, ana zargin tsohon shugaban dakarun IRT da saida kason NDLEA na kilo 5 a kan Dala 61, 400 (kimanin Naira miliyan 25 a kudin Najeriya).

Hana doka tayi aiki

Har ila yau akwai zargin yunkurin hana doka tayi aikinta a kan DCP Kyari. NDLEA ta ce jami’in ya yi kokarin sa jami’inta ya boye hodar iblisin da aka karbe.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Babu jami'anmu cikin masu harkallar miyagun kwayoyi, inji NDLEA

Me dokar kasa ta ce?

Sashe na biyu na dokar NDLEA ta ce a yankewa duk wani wanda aka samu da hannu wajen aikata laifin hukuncin daurin shekaru 15 zuwa 25 a gidan yari.

Rahoton HeadTopic ya bayyana cewa a karkashin dokokin Najeriya, hukuncin daurin rai da rai ake yi wa duk wanda aka tabbatar ya yi safara ko ya saida kwaya.

Wanda aka samu ya taba kwaya kuwa zai gamu da daurin da bai zarce shekaru 25 a kurkuku ba. Sannan wanda aka kama zai rasa duka dukiyoyin da ke hannunsa.

Kanin Abba Kyari ya shiga ciki?

Binciken da ‘Yan Sanda suka gudanar a kan Abba Kyari ya nuna akwai hannun wani ‘danuwansa a badakalar da ke wuyansa bayan an gano an rika aika masa kudi.

Rahoton da mu ka fitar a makon nan ya tabbatar da cewa Ramon Abass wanda aka fi sani da Hushpuppi da mutanensa sun aikawa kanin Kyari kudi N235, 120, 000.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel