Abba Kyari: Babu jami'anmu cikin masu harkallar miyagun kwayoyi, inji NDLEA

Abba Kyari: Babu jami'anmu cikin masu harkallar miyagun kwayoyi, inji NDLEA

  • Rundunar NDLEA ta yi martani ga jami'an 'yan sandan Najeriya game da batun harkallar Abba Kyari
  • Wannan martani na zuwa ne bayan da rundunar 'yan sanda tace ya kamata a bincike jami'an NDLEA a lamarin Kyari
  • Martanin na NDLEA ya bayyana hujjojin da hukumar ta dogara dashi cewa Kyari da tawagarsa ne 'yan harkallar kwaya

Abuja - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta yi martani ga zargin rundunar 'yan sandan Najeriya cewa a bincika ko akwai 'yan harkallar kwaya a cikin jami'an NDLEA, inji rahoton TheCable.

Wannan zargi na 'yan sanda na zuwa ne jim kadan bayan da NDLEA ta ce tana neman DCP Abba Kyari bisa zarginsa da shiga harkallar miyagun kwayoyi.

Batun tona asirin Abba Kyari
Abba Kyarin ne dai: NDLEA ta yi martani ga 'yan sanda cewa akwai 'yan harkalla a cikinsu | Hoto: tvcnews.tv
Asali: Twitter

Idan baku manta ba, an kama Kyari da wasu jami'an 'yan sanda hudu da ake zargin 'yan tawagar wasu masu safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa ne.

Kara karanta wannan

Waiwaye: Can baya, hoton lokacin da Abba Kyari ke da'awar yaki da shan kwayoyi

Rundunar ‘yan sandan ta ce bincike ya nuna cewa tawagar masu safarar miyagun kwayoyin ta kasa da kasa tana da “dangantaka mai karfi” da wasu jami’an NDLEA a filin jirgin sama na Enugu inda ta bukaci NDLEA ta binciki jami’anta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani abu mai kama da martani ga ‘yan sanda, NDLEA, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ta ce hukumar ta jajirce wajen gudanar da bincike kan gano shaidu kuma ba zai hana ta gano gaskiya ta bi ta ba.

Sanarwar ta warware bayanan da ke yawo cewa, hujjojin da hukumar NDLEA ta samu daga Abba Kyari da kuma ASP James Bawa ya nuna cewa, tawagar ta Abba Kyari ne ke kokarin kulla harkallar.

Hujjojin NDLEA

Sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga Daily Trust ta yi karin bayani kamar haka:

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA ta yiwa IGP martani

“Ku tuna cewa bayan da NDLEA ta nemi Kyari da sauran 'yan tawagarsa don a yi musu tambayoyi, ‘yan sanda sun yi musu tambayoyi, daga baya an mika su tare da rahoton tambayoyin da aka yi musu.
"A cewar rahoton binciken 'yan sanda, ASP James Bawa a cikin bayanan da ya yi ga 'yan sanda ya nuna cewa "wani dan kwarmato bayanai mai suna IK daga Brazil ya kira shi ya gaya masa cewa wani dan aike da kwayoyi zai iso a cikin jirgin Ethiopian Airlines a Enugu.
"Ya kara da cewa wani mai nuni daga IK, dan kasar Brazil ya gana da shi da misalin karfe 14:20 a ranar 19 ga Janairu, 2022 a wajen filin jirgin sama kuma ya nuna masa hoton dan aiken.
“Daga baya, sun hangi wanda ake zargin yayin da ya fito daga tashar jirgin bayan an kama shi tare da wani abokinsa.
“Babu shakka abin da ke sama ya tabbatar da wanda yake tare da tawagar da kuma tsarin aikin su."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: NDLEA Ta Fara Yi Wa Abba Kyari Zafafan Tambayoyi a Ofishinta

Wannan sabon zargi dai na zuwa ne ‘yan watanni bayan da hukumar binciken manyan laifuka ta kasar Amurka (FBI) ta tuhumi Kyari da hada baki da Hushpuppi, dan damfarar kasa da kasa, a wata badakalar dalar Amurka miliyan 1.1.

Yadda IGP da Marwa suka gana, suka shirya yadda za a damke Abba Kyari da mukarrabansa

A wani labarin, sabon labari ya bayyana a kan yadda sifeta janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba da shugaban hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA), Birgediya janar Buba Marwa, suka hadu a hedkwatocin tsaro dake Abuja.

Sun yanke shawarar yadda za su bullo wa lamarin kwamandan hukumar binciken sirri na 'yan sanda da aka dakatar, DCP Abba Kyari, bisa hannunsa a harkallar safarar hodar iblis mai nauyin kilogram 25.

Bayanin yazo ne bayan kwana daya da 'yan sanda suka dakatar da duk wasu rassa na IRT na jihohin dake fadin kasar, wanda hakan ya biyo bayan kama DCP Kyari da aka yi.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Sunayen manyan 'yan sanda 5 da aka kwamushe tare da mikawa NDLEA

Asali: Legit.ng

Online view pixel