Isa Pantami ko albashi bai karba hannun jami'ar FUTO, ASUU ta shiga taitayinta - MURIC

Isa Pantami ko albashi bai karba hannun jami'ar FUTO, ASUU ta shiga taitayinta - MURIC

  • Kungiyar MURIC ta yi kira ga ASUU ta shiga taitayinta ta daina shiga sharo ba shanu kan abinda ba tada hurumi a kai
  • Wannan ya biyo bayan watsi da farfesancin Ministan sadarwa, Malam Isa Ali Pantami da ASUU tayi
  • MURIC tace yaushe ASUU ta zama hukuma dake da hurumin rusa hukuncin da majalisar jami'a tayi

Legas - Kungiyar kare hakkin Musulmai MURIC ta caccaki kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU bisa watsi da nadin Ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami, matsayin Farfesa.

MURIC ta bayyana bacin ranta ne ta bakin Diraktanta, Farfesa Ishaq Akintola, ranar Talata, 15 ga Febrairu, 2022.

Zaku tuna cewa ASUU ta yi watsi da matsayin Farfesa da aka bai wa ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dakta Isa Pantami.

Kara karanta wannan

Ba zan yi tsokaci kan matsayar ASUU a kan farfesanci na ba, Pantami

Kungiyar, bayan taron majalisar zartaswa ta da ya gudana ranar Litinin, ta bayyana baiwa Pantami Farfesa a matsayin, "karan tsaye ga doka."

MURIC
Isa Pantami ko albashi bai karba hannun jami'ar FUTO, ASUU ta shiga taitayinta - MURIC Hoto: FMCDE
Asali: Twitter

Akintola yace:

"ASUU ba tada hurumin haramta nadin da jami'a tayi da izinin kwamitin kara matsayi na majalisar zartaswar jami'ar."
"Me ASUU ke kokarin yi? Menene matsalarsu? ASUU ba tada hakkin kwace ikon jami'a."
"Wannan wuce gona da iri ne. Ya kamata ASUU ta san iyakarta. Shin akwai wani sashen kundin tsarin mulkin ASUU da ya bata damar take nadin da jami'o'i suka yi. Wannan fito-na-fito ne. Babu wata-wata."
"Bayan haka, aikin Farfesa Pantami a FUTO fisabilillahi yake yi kuma bai karban kudi kuma akwai daman hakan a aikin gwamnati. Hakazalika Ministan ba da rashin sani da izinin Shugaban kasa yayi ba."

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Minista ya yi martani kan tafiyar ASUU yajin aiki, za a biya musu bukata

Jami'ar FUTO ta fusata, ta ce ta maka ASUU a kotu

Shugabar jami’ar tarayya dake Owerri (FUTO), Farfesa Nnenna Oti, ta ce hukumar jami'ar ta garzaya kotu saboda kin amincewa da karin girma da ta yiwa Dakta Isah Ibrahim Pantami a matsayin Farfesa a fannin tsaro na Intanet.

Hakan ya biyo bayan barazanar da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta yi na kakabawa FUTO takunkumi kan amincewa da Pantami a matsayin farfesa yayin da yake ci gaba da rike mukami a matsayin minista.

Oti ta shaidawa jaridar The Nation jiya Litinin cewa hukumar jami'ar ta garzaya kotu a kan lamarin, inda ta ce duk wani sharhi ko tattaunawa a kai, tozarci ne kawai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel