Yanzu-yanzu: Nnamdi Kanu ya kusa makancewa, Lauyansa ya bayyanawa kotu

Yanzu-yanzu: Nnamdi Kanu ya kusa makancewa, Lauyansa ya bayyanawa kotu

Abuja - Sabon lauyan da ke tsayawa shugaban kungiyar yan tawayen IPOB Nnamdi Kanu a kotu, Chief Mike Ozekhome(SAN), ya bayyana cewa ciwon idon Kanu ya tsananta.

Mike Ozekhome, ya bayyana hakan yayin zaman kotu na ranar Laraba, 16 ga Febrairu, 2022, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, idan ba'a dau matakin gaggawa ba, Nnamdi Kanu zai makance a hannun hukumar DSS.

Kanu na cigaba da gurfana gaban Alkali Binta Nyako ta babbar kotun tarayya dake Abuja.

Ana zargin Kanu da laifuffuka daban-daban da suka hada da na cin amanar kasa da ta’addanci, laifukan da ake zargin ya aikata a kacaniyar aware don kafa kasar Biafra

Yanzu-yanzu: Nnamdi Kanu ya kusa makancewa, Lauyan ya bayyanawa kotu
Yanzu-yanzu: Nnamdi Kanu ya kusa makancewa, Lauyan ya bayyanawa kotu
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mike Ozekhome, ya ja hankalin alkali mai shari’a, Binta Nyako kan irin matsalolin da suke fuskanta a kokarin kai sabbin tufafi ga shugaban kungiyar ta IPOB a tsare a Abuja.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An yi cacar baki tsakanin mai Shari'a da Nnamdi Kanu kan tufafinsa

Lauyan DSS zuwa yace ba zai yiwu ya ci gaba da sanya tufafi masu dauke da alamar zaki ba.

A jawabinsa, ya shaidawa kotu cewa:

"Mai Shari'a, tufafin da aka kawo wa wanda ake kara akwai hoton kan zaki a jiki, kuma wanda ake kara (Mr Kanu) ba zai yiwu ya sanya tufafi da kan zaki ba."

Yayi karin bayani da cewa, “tufafi da kan zaki ya saba wa ka’idojin aiki” na SSS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel