Hotunan takalmi mafi tsada a duniya ya bayyana a birnin Dubai, kudinsa N8bn

Hotunan takalmi mafi tsada a duniya ya bayyana a birnin Dubai, kudinsa N8bn

  • A Oktoban 2021, an bayyana takalmi mafi tsada a duniya karo na farko a birnin Dubai, kasar UAE
  • Wani mai hada takalama dan kasar Italiya, Antonio Vietri ne ya hada takalmin da aka yiwa kwalliya da lu'u-lu'u
  • A 2017, mutumin ne ya kera wani takalmi da gwal karat 24 na kudi kimanin milyan goma sha hudu

Wani mai hada takalma dan kasar Italiya, Antoni Vietri, ya karya tarihi inda ya hada wani sabon takalmi mafi tsada a fadin duniya, wanda farashinsa ya kai N8.2 billion (Dh73 million).

A cewar jaridar, The National News, an hada dunduniyar takalmin da zinari, karat na lu'u-lu'u da kuma wani karamin dutse da aka gano a kasar Argetina a shekarar 1576.

Kara karanta wannan

'Yan siyasa 4 da su ka rike Minista a mulkin Jonathan, yanzu su ne Gwamnonin jihohinsu

An yiwa dunduniyar kwalliya kamar shahrarren ginin Burj Khalifa.

Talkalmi
Hotunan takalmi mafi tsada a duniya ya bayyanaa birnin Dubai, kudinsa N8bn Hoto: AFP
Asali: UGC

Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan takalmi:

Shukhrana Yusif yace:

"Ana tashi sama in a saka takalmin?"

Arfat Yusif yace:

"Wannan almubazzaran cine."

Sã'ēēd Abdûllãh Sõbã:

WANNAN MUMMUNAR TAKALMIN SHINE 8bn. Saura kuma wani yace haushin rashi ne

Asiya Usman tace:

Indai ba aljannah zaya kaimu ba meye abin so a jiki? tomu silifa ya ishemu rayuwar diniyar ga!!!

Helena Robert:

Tsohuwar ministar Najeriya ce kawai zata iya siya a ƙasar
Duk wanda bai yarda ba hassada ce

Asali: Legit.ng

Online view pixel