'Yar Najeriya ta dawo gida daga Ingila bayan shekaru 25, ta tarar mai haya ya sayar da gidanta

'Yar Najeriya ta dawo gida daga Ingila bayan shekaru 25, ta tarar mai haya ya sayar da gidanta

  • Wata mata da aka kora daga Ingila bayan shekaru 25 ta zama abin tausayi a jihar Legas saboda rashin muhalli
  • Florence Owanogo ta dawo gida Najeriya kawa ta tarar mai hayan da ta baiwa amanan gida mai ya sayar da gidan
  • Matar tace ta kaiwa yan sanda kara amma sai yan sanda suka garkameta maimakon bincike kan maganarta

Wani mutumi ya bayyana arangamarsa da wata mata mai suna Florence Owanogo mai shekaru 65 wacce ta ke kwana a kan titin 5th Avenue, 51 road Festac, Legas saboda rashin muhalli.

Matar tace an korota Najeriya daga Ingila bayan shekaru 25 amma ta tarar an sayar da gidanta daya tilo da ta mallaka a Najeriya.

Wanda ya bada labarin a Tuwita @Diixixme yace da farko yayi tunanin na da tabin hankali ne amma ya yanke shawarar tattaunawa da ita daren Laraba, 9 ga Febrairu.

Kara karanta wannan

Dirama ta ɓarke a Kotu yayin da Amarya ta yi ikirarin Ango ya danna mata saki uku a waya

A cewarsa, a lokacin ta bashi labarin halin da ta shiga.

Festac
'Yar Najeriya ta dawo gida daga Ingila bayan shekaru 25, ta tarar mai haya ya sayar da gidanta Photo Credit: Twitter/@Diixixme, Kola Sulaimon
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kai kara wajen yan sanda

Yace matar tayi masa bayanin yadda ta kai kara wajen yan sanda amma daga karshe an hada baki da yan sandan kuma suka garkameta.

Hakan yasa ta hakura ta fara kwana bakin titi.

Yace:

"Tayi shekaru 25 a UK amma kalli irin muguntar da akayi mata."

Yadda ya hadu da ita

@Diixixme ya bayyanawa Legit cewa ya hadu da matar ne lokacin da ta tsinci wayarsa kuma ta bashi.

Yace:

"Ban santa ba. Na batar da wayata kuma ita ta tsinta kuma ta kira ni. Abin mamaki ko waya ba ta da shi."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel