So Makaho ne: Jami'ar Najeriya ta sallami ɗalibin 400-Level saboda nuna wa budurwarsa kauna

So Makaho ne: Jami'ar Najeriya ta sallami ɗalibin 400-Level saboda nuna wa budurwarsa kauna

  • Wani ɗalibin Najeriya ya rasa damar karatunsa a jami'ar Ilorin saboda ya rubuta wa budurwarsa jarabawa
  • Rahoto ya nuna cewa Ɗalibin ya je dakin zana jarabawa domin taimaka wa budurwarsa ta rubuta Kwas ɗin GNS112 amma aka damƙe shi
  • Labarin Saurayin ya ja hankalin yan Najeriya da dama, inda suka maida masa martani, wasu na ganin ba shi da waye wa

Ilorin - Yunkurin wani ɗalibi na taimaka wa budurwarsa a ɗakin jarabawa ya yi sanadin kawo karshen karatunsa a jami'ar Ililorin (UNILORIN).

Jami'ar ta sallami ɗalibin daga karatun da yake yi yayin da ta kama shi dumu-dumu yana rubutawa budurwarsa jarabawa.

Jami'ar Ilorin
So Makahone: Soyayya ta ɗibi wani Ɗalibin 400-Level ya zauna wa Budurwarsa jarabawa, Jami'a ta yanke hukunci Hoto: UNILORIN
Asali: UGC

Ta ya lamarin ya faru?

A labarin da muka samu, Ɗalibin ya halarci ɗakin jarabawa domin rubutawa budurwarsa jarabawar aji ɗaya GN112, amma rana ta baci aka kama shi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗalibar 200-Level a Jami'ar Najeriya ta faɗa cikin Masai, Allah ya mata rasuwa

Da yake bayyana lamarin a shafin Twitter, @_Mayorbaby ya ce:

"UNILORIN ta sallami wani ɗalibin aji hudu yau sabida ya je zana wa budurwarsa jarabawar GN112. Mutumin da sauran yan watanni ya kammala karatunsa. Ba yan ƙauye kaɗai ke kauyanci ba, wannan dai ya yi shirme."

Martanin yan Najeriya

Yan Najeriya sun yi rubdugu a wajen maida martani a labarin, inda mafi yawansu ke ɗora laifi kan ɗalibin da cewa ya nuna ƙauyanci. Wasu kuma na ganin hukuncin ya yi tsauri.

@MarkOtabor yace:

"Hukuncin ya yi tsauri, a ra'ayi na kamata ya yi a dakatar da shi na shekara ɗaya domin irin wanna ka iya sanya shi ya kashe kansa. Wata kila budurwan ba ta da lafiya ne, ko da ba haka bane ina ganin babu adalci a kore shi."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Duk jam'iyyar da ta tsayar da ɗan arewa ba zata samu nasara ba, Gwamnan APC

@Sbaton24 yace:

"To wa zaka zarga yanzu? Kai wane irin masoyi ne da zaka zauna wa ɗalibar aji ɗaya jarabawa. Idan har ba zata iya Kwas ɗin gabatarwa ba, me ya kawo ta makaranta. Wannan ba so bane hauka ce kawai."

@MarthaOnoriode yace:

"Ba wanda zai iya wannan ko da ma matarsa ce ta aure ballanta wai budurwa."

A wani labarin kuma Jaruma Sadiya Haruna, Rabi Isma'ila da wasu Jarumai Mata 2 da Kotu ta ɗaure a Kurkuku

A kwanan nan ne wata Kotun Majistire dake jahar Kano ta ɗaure Jaruma Sadiya Haruna na tsawon watanni 6 a gidan Yari.

Hakan yasa muka tattaro muku jerin Jaruman Fim mata a Najeriya da Kotu ta taɓa yanke musu hukunci ɗauri bayan kama su da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel