'Yan bindiga sun halaka jagoran al'ummar musulmi a Delta bayan ya yi sallar Isha'i a masallaci

'Yan bindiga sun halaka jagoran al'ummar musulmi a Delta bayan ya yi sallar Isha'i a masallaci

  • Mahara da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne sun kashe Sakataren Kwamitin Koli ta Harkokin Addinin Musulunci reshen Jihar Delta, Musa Ugasa
  • Yan bindigan sun bude wa Musa wuta ne a Uloho Avenue, Jihar Delta da dare yayin da ya ke komawa gida bayan yin sallar Isha'i a wata masallaci da ke kusa da unguwarsu
  • Mumakai-Unagha, Shugaban al'ummar musulmi a jihar kuma tsohon mai neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar, APC, ya yi tir da kisar Musa

Jihar Delta - Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun halaka Sakataren Kwamitin Koli ta Harkokin Addinin Musulunci reshen Jihar Delta, Musa Ugasa.

Vanguard ta ruwaito cewa an yi masa kisar gillar ne a yayin da ya ke dawowa daga masallaci bayan yin Sallar Isha'i a Uloho Avenue, Ughelli, Jihar Delta.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

An kashe jagoran al'ummar musulmi a Delta bayan ya yi sallar Isha'i a masallaci
Yan bindiga sun kashe jagoran al'ummar musulmi a Delta bayan ya yi sallar Isha'i a masallaci. Hoto: Vangaurd
Asali: Twitter

Mai magana da yawun kungiyar ta musulmi, Issa Edogamhe, wanda ya tabbatar da kisar gillar ya ce:

"An kai masa hari ne a lokacin da ya ke dawowa daga wani masallaci a nan kusa inda ya tafi sallar Isha'i. An kashe shi ne a kan titin Uloho Avenue, Ughelli."

Hakazalika, Shugaban al'ummar musulmi a jihar kuma tsohon mai neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Mumakai-Unagha, ya bayyana kisar da aka yi wa Musa a matsayin abin takaici, rahoton Vanguard.

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Kara karanta wannan

Hana sa Hijabi a Kwara: Ba zamu lamunci wannan rainin hankalin ba: Kungiyar Musulmai

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel