Zulum ya nemawa matasa 3200 hanyar neman abinci da Motoci da Keke Napep 600

Zulum ya nemawa matasa 3200 hanyar neman abinci da Motoci da Keke Napep 600

  • Gwamnatin jihar Borno ta dauki mataki domin ta samu ta rage adadin masu zaman kashe wando
  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya raba Keke Napep da motoci da-dama ga matasa fiye da 3000
  • Za a rika amfani da motocin Toyota Corolla LE domin haya a birnin Maiduguri da kewayen Borno

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa, Babagana Umara Zulum ya raba kanana da manyan motoci da keke napep ga matasa 3, 200 da ba su da aikin yi.

Punch ta ce gwamnatin Mai girma Babagana Umara Zulum tayi wannan aiki ne domin a saukaka tafiye-tafiye a Maiduguri da yankunan Jere da kuma Konduga.

Gwamnan ya raba abubuwan hawa da suka hada da mota kirar Toyota Corolla LE har 100 da za a rika amfani da su a matsayin motocin haya a cikin birnin jihar.

Kara karanta wannan

Ba na son cin haram, ana biya na kudin da ban yi aiki ba, Hadimin gwamna ya yi murabus

Bayan haka an rabawa matasan da ke zaman kashe-wando babura har 500 masu kafafu uku wadanda aka fi sani da ‘Keke NAPEP’ saboda daukar fasinjoji.

Gidan TVN ta ce gwamnatin jihar Borno ta kuma raba manyan motocin haya kirar Ashok Leyland buses guda 10. Kowace mota za ta iya daukar akalla mutane 10.

Motoci da Keke Napep
An raba abubuwan hawa a Borno Hoto: @BornoYoung
Asali: Twitter

Isa Gusau ya yi jawabi

An raba motocin ne a filin Ramat Square da ke Maiduguri a jihar Borno a ranar Alhamis, 3 ga watan Fubrairu 2022 kamar yadda hadimin gwamna ya yi jawabi.

Isa Gusau ya fitar da jawabi da yawun bakin Gwamna Zulum da ya yi wa take da “Mass transit: Zulum launches 610 taxis, tricycles, buses in Maiduguri” a jiya.

Gusau ya ce kamfanin Borno Express Transport Corporation for intercity services zai kula da motocin.

Kara karanta wannan

Zulum: Boko Haram za ta zama tamkar wasan yara idan aka bari ISWAP ta girma

Yadda aka yi tsarin

Matasa masu neman aikin yi hudu za su raba kowane babur. Hakan nufin mutane 2000 za su samu hanyar neman na abinci daga wadannan Keke Napep da aka raba.

Mutum biyu za su raba kowace mota inda a karshe za su raba duk ribar da aka samu wajen aiki.

Baya ga mutum 2200 da za su rika amfani da motoci da baburan wajen haya, Zulum ya ware N50m ga direbobin Keke Napep 1000 da ba za su amfana da tsarin ba.

Tattalin arziki na cikin matsala

Shugaban Majalisar dattawa na kasa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya koka a kan makudan tiriliyoyin kudin da gwamnati ta ke batarwa duk shekara a biyan bashi.

A makon nan aka ji Farfesa Nazif Abdullahi Darma ya ce duk shekara ana samun karin mutane akalla miliyan shida a Najeriya, adadin ya na karuwa da 500, 000 a wata.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum

Asali: Legit.ng

Online view pixel