Gwamnati ta yadda ana cikin matsala bayan hango tulin bashin da ke wuyan Najeriya

Gwamnati ta yadda ana cikin matsala bayan hango tulin bashin da ke wuyan Najeriya

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan ya koka a kan bashin da Najeriya take biya
  • Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya ce abin da gwamnati ke batarwa wajen biyan bashi ya kai $4tr
  • A wajen wani taro Lawan ya zargi kungiyoyin haraji da hannu wajen sukurkucewar tattalin arziki

Abuja - A wajen wani taro na CITN, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan ya tabbatar da cewa akwai bashi mai yawa a kan gwamnatin tarayya.

Jaridar Sun News ta rahoto Sanata Ahmad Ibrahim Lawan yana cewa bashin da Najeriya ke biya ya karu daga Dala tiriliyan 2.5 a 2019 zuwa Dala tiriliyan 4.1 a yau.

Shugaban majalisar dattawan ya yi jawabi na musamman yayin da kungiyar kwararrun malaman haraji watau CITN ta ke bikin cika shekaru 40 da kafuwa.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Sule Lamido ya ce Tambuwal ne ya fi dacewa ya gaji Buhari, ya fadi dalili

Ahmad Ibrahim Lawan ya ce an samu karin Dala tiriliyan 1.6 a abin da gwamnati take kashewa wajen biyan bashi. An samu wannan kari a cikin kusan shekara biyu.

Abin da hukumomin karbar haraji da nemawa gwamnatin tarayya kudin shiga suka iya tatsowa a shekarar 2020 bai wuce Dala tiriliyan 8 ba a cewar Sanata Lawan.

Ahmad Ibrahim Lawan
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan Hoto: TheSenatePresident
Asali: Facebook

Nazif Abdullahi Darma ya wakilci Lawan

Farfesa Nazif Abdullahi Darma mai taimakawa shugaban majalisar wajen harkar tattalin arziki shi ne ya wakilce shi a wajen wannan biki da aka shirya a garin Abuja.

A madadin Lawan, Farfesa Nazif Darma ya fito karara ya zargi kungiyar CITN da taimakawa wajen tabarbarewar tattalin arziki, ya ce ba za a ce babu hannunsu ba.

“A shekarar bara bashin da ake biya ya kai $11. 93tr. A yau mu na da gibin kusan Dala biliyan 500 na gina abubuwan more rayuwa.”

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

“Kasar nan ba za ta shiga cikin wannan matsala ba idan ba tare da sa hannun manya irinsu CITN da sauran kungiyoyin ma’aikata ba.”

- Farfesa Nazif Abdullahi Darma

Farfesan ya ke cewa duk shekara sai an samu karin mutane kimanin miliyan shida a Najeriya, a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar yake motsawa da kasa da 4%.

Sauran wadanda suka samu halarta kuma suka yi jawabi a wajen taron sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ta bakin Zainab Shamsuna Ahmed.

Sababbin nadin mukami

A ranar Laraba ne ake jin Fadar shugaban kasa ta aikawa majalisar dattawa takarda ta na neman a nada kwamishinoni a hukumar NERC mai kula da wutar lantarki.

Mai girma Muhammadu Buhari ya kuma nada Darekoci a Hukumomin Nigerian Midstrea & Downstream Petroleum Regulatory Authority dahukumar nan ta NDIC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel