Shugaba Buhari ya kawo duk wani cigaba da mutane ke bukata, Abu ɗaya ya rage yan Najeriya su yi, Minista

Shugaba Buhari ya kawo duk wani cigaba da mutane ke bukata, Abu ɗaya ya rage yan Najeriya su yi, Minista

  • Karamin ministan ilimi a Najeriya ya yi ikirarin cewa shugaba Buhari ya gina muhimman ayyuka ga yan Najeriya
  • Chukwuemeka Nwajiuba, yace yanzun ya rage wa yan Najeriya su yi amfani da wannan damar wajen haɓaka bangaren kirkira
  • A cewarsa babu kasar da zata cigaba matukar ba ta samar da kayayyaki da zata yi amfani da su har ta fitar

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi duk wani abu da zai iya wajen haɓaka da kawo cigaba Najeriya, amma ƙalubalen shi ne yan Najeriya su farga su amince da cigaban ƙasar su.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, shi ne ya bayyana haka a wurin taron ilimi da ya gudana a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda Dailytrust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Halin da ake ciki kan batun ɗan uwan Goodluck Jonathan da yan bindiga suka sace

Chukwuemeka Nwajiuba
Shugaba Buhari ya kawo duk wani cigaba da mutane ke bukata, Abu ɗaya ya rage yan Najeriya su yi, Minista Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Nwajiuba, yace babu dalilin da zaisa yan Najeriya su koma gefe ba tare da bada gudummuwa ba, domin shugaba Buhari ya kafa tubali mai ƙarko.

Ministan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun ce ba zai taɓa yuwu wa a tattara asusun gwamnati wuri ɗaya ba, shugaba Buhari ya fara kuma ya maida Asusu ya zama ɗaya. Sun ce Najeriya ba zata iya harkokin Banki da BVN ba, yanzin da ita ake amfani."
"Sun ce Najeriya ba zata iya komawa tsarin biyan albashi guda ɗaya ba IPPIS domin magance ma'aikatan bogi, amma Buhari ya maida kowane ma'aikaci kan IPPIS."

Ministan ya ƙara da cewa duk abin da suka ce Najeriya ba zata iya yi bq saboda cin hancin da ya dabai-bayeta, shugaba Buhari ya ɗauka a kafaɗarsa ya zartar da su.

A cewarsa, duk da suka da zagi da yan Najeriya ke masa, Buhari ya dage ya cije har tabbatar ya tsaya da ƙafarsa.

Kara karanta wannan

Mutanen Twitter sun ba PDP shawarar ta tsaida Peter Obi/Kwankwaso a zaben 2023

Abu ɗaya da ya rage yan Najeriya su yi

Nwajiuba yace yayin da yan Najeriya suka gaza kirkirar abu su fitar da shi waje sai kirkiro matsaloli shiyasa, "Muke da matsalolin da suka taso daga Najeriya, amma ba mu samar da kayayyakin yan Najeriya."

"Duk ƙasar da bata kirkire-kirkire ba zata yi ƙarko ba, domin kowace ƙasa sai ta nemi abin da zata dogara da shi."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun yi kaca-kaca ofishin yaƙin neman zaɓen Ministan Buhari

Mutane sun shiga tashin hankali a jihar Osun yayin da wasu yan ta'adda suka kai hari ofishin yaƙin neman zaɓen Rauf Aregbesola.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda maharan suka tada wuta ta hanyar buɗe wa wata Turansufoma wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel