Hukumar NBC ta haramta shirin 'Idon Mikiya' na tashar Vision Fm, ta cisu tarar N5m

Hukumar NBC ta haramta shirin 'Idon Mikiya' na tashar Vision Fm, ta cisu tarar N5m

  • Gwamnatin tarayya ta dakatad da shirin Idon Mikiya na tashar Vision FM bisa saba dokar kasa
  • Hukumar NBC ta zargi gidan rediyon Vision da laifin tattauna lamarin da ya shafi tsaro wanda hakan bai dace ba
  • NBC ta ce tattauna mas'aloli irin wannan fallasa sirrukan gwamnati ne kuma ka iya zama matsala

Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin NBC ta dakatad da haska shirin Idon Mikiya na tashar VisionFM kan laifin tattauna tsawaita nadin shugaban hukumar leken asirin kasa NIA, Rufa'i Abubakar.

A wasikar da NBC ta turawa shugaban tashar VisionFM ranar Laraba, tace ta sanyawa gidan rediyon takunkumi ne saboda illar maganganun da sukayi a shirin 'Idon Mikiya' a ranar 5 ga Junairu, 2022.

Hukumar NBC ta haramta shirin 'Idon Mikiya' na tashar Vision Fm, ta cisu tarar N5m
Hukumar NBC ta haramta shirin 'Idon Mikiya' na tashar Vision Fm, ta cisu tarar N5m

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya aikawa Majalisa sunayen sababbin mukaman da ya nada a Gwamnati

NBC tace wannan ya sabawa sashe 39 (3) (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya da ta haramta tattauna lamuran tsaro da hukumominta.

A cewar wasika:

"Abubuwan da kuke tattaunawa, ciki har da nadi a hukumar leken asirin Najeriya (NIA) ya sabawa sashe 39 (3) (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya sanya takunkumi kan abubuwan da suka shafi lamuran tsaro."

Hukumar ta ci Vision FM tarar N5 million kuma ta dakatad da shirin Idon Mikiya na tsawon watanni shida.

NBC tace ana bayyana sirrukan gwamnati a shirin kuma hakan na da illa da tsaro.

A watan Disamba, shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin shugaban NIA duk da cece-kucen da akeyi.

Lai Mohammed, ministan labarai da al’adu ya yi jan hankali a kan yada labaran karya

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari gidan shugaban ASUU na Jami'ar Gusau, sun sace 'yan uwansa 5 da makwabcinsa

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya gargadi al’umman kasar a kan yada labaran karya, inda ya ce hakan na iya haddasa yakin duniya na uku.

Mohammed ya fadi hakan ne a ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan labarai domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa na 2022.

Ministan ya ce sigar da ake amfani da ita wajen yada labarai a yau ta canza matuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel