‘Yan bindiga sun aika mutane 1, 192 barzahu, sun dauke 3, 348 cikin shekara 1 a Kaduna

‘Yan bindiga sun aika mutane 1, 192 barzahu, sun dauke 3, 348 cikin shekara 1 a Kaduna

  • Alkaluman da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar ya nuna ‘yan bindiga sun kashe mutane fiye da 1, 000
  • Rahoton da aka fitar ya nuna an yi garkuwa da Bayin Allah fiye da 3, 000 a Kaduna a shekarar bara
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya bayyana wannan a wani rahoto da ya gabatar dazu

Kaduna - Akalla mutane 1, 192 suka mutu a hannun ‘yan bindiga, sannan kuma an yi garkuwa da wasu mutum 3, 348 a jihar Kaduna a shekarar da ta wuce.

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wadannan alkaluma a makon nan.

Wannan bayani yana cikin rahoton harkar tsaro da aka fitar daga watan Junairu zuwa Disamban 2021 wanda kwamishinan tsaron cikin gida ya gabatar dazu.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Mista Samuel Aruwan ya gabatar da wannan rahoto ne ga Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a ranar Talata, 1 ga watan Fubrairu 2022.

Samuel Aruwan ya ce an samu mutuwar mutane 720 a yankin tsakiyar Kaduna a sakamakon garkuwa da mutane, rikicin kabilanci, da sauran tashin-tashina.

Blueprint ta ce wadanda aka kashe sun hada da maza 1, 038, mata 104 da kananan yara 50. Alkaluman sun nuna an samu karuwar mace-mace da sata a bana.

Kaduna
Taron majalisar tsaro a Kaduna Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Har ila yau an tabbatar da satar shanu 10, 261 a shekarar baran, adadin satar da aka yi ya nunku.

Kwamishinan yake cewa an samu mace-mace har 406 a sakamakon rikicin garuruwa da satar mutane a yankin kudancin jihar Kaduna a shekarar da ta wuce.

Kiran Mai girma Nasir El-Rufai

Kara karanta wannan

Yan sanda sun ceto tsohon kansilan da yan bindiga suka sace a Nasarawa

Gwamna Nasir El-Rufai ya ce alkaluman da aka fitar sun nuna cewa kusan a kullum sai ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane tara a jihar Kaduna a shekarar 2021.

El-Rufai ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da sansanin sojoji a Arewa maso yamma makamancin wanda aka kafa domin yakar ‘yan Boko Haram.

“Kirkirar irin wannan sansani zai bada dama a bullowa sha’anin yakar rashin tsaro gada-gadan a jihohi shida da abin ya shafa.”
“Wannan zai taimakawa sojoji, ‘yan sanda, dakarun SS, ‘yan banga da sauran ‘yan sa-kai wajen yakar masu tada kafar-baya.”

- Malam Nasir El-Rufai

Hari a Zangon Kataf

A ranar Litinin ne aka ji cewa miyagun ‘Yan bindiga sun kuma shiga yankin Kurmin Masara a karamar hukumar Zangon-Kataf, a jihar Kaduna sun yi ta'adi.

Wannan ne hari na biyu da ‘Yan bindiga suka kai a kauyen a cikin kwanaki biyu da suka wuce.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Asali: Legit.ng

Online view pixel