Buhari ya soke zuwa Zamfara ne saboda tsoron yan ta'adda, PDP ta magantu

Buhari ya soke zuwa Zamfara ne saboda tsoron yan ta'adda, PDP ta magantu

  • Jam'iyyar adawa PDP ta yi watsi da uzurin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, na fasa zuwa Zamfara
  • PDP ta ce idan yanayin hazo a sararin samaniya ya hana jirgi tashi, me zai sa shugaban ba zai tafi a cikin mota ba
  • A cewar PDP, rashin zuwa Buhari Zamfara wata babbar alama ce ta gazawar gwamnatin APC

Abuja - Biyo bayan soken zuwansa Gusau, babban birnin jihar Zamfara ranar Alhamis, jam'iyyar hamayya PDP ta caccaki shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Punch ta rahoto PDP na cewa shugaban ya fasa zuwa Zamfara ne saboda halin rashin tsaro da yan bindiga suka jefa jihar a ciki.

Jam'iyyar ta nuna cewa inda Buhari ya so zuwa Zamfara da ya bi ta hanyar ƙasa, amma, ''yana tsoro saboda ba shi da tabbacin tsaro da kuma lalacewar da hanyoyi suka yi ƙarƙashinsa."

Kara karanta wannan

Rayuwar Aure: Kotu ta datse Igiyoyin auren wata mata saboda mijin ya faɗa soyayya da kare

Shugaba Buhari
Buhari ya soke zuwa Zamfara ne saboda tsoron yan ta'adda, PDP ta magantu Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, shi ne ya faɗi haka a wata sanarwa mai taken, "Rashin tsaro: PDP ta yi hannun riga da matakin Buhari na fasa zuwa Zamfara."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babbar jam'iyyar hamayya ta yi watsi da uzurin da shugaba Buhari ya bayar na ƙin zuwa Zamfara cewa 'Yanayi ba kyau,' bayan akwai zaɓin tafiya ta kan titi.

Vanguard ta rahoto A sanarwan, PDP ta ce:

"Muna da tambaya, shin shugaban ƙasa ya soke zuwa Zamfara ne saboda tsoron ta'addanci? Shin shugaban ƙasa, Janar ɗin soja, da dukkan dakarun tsaro a ƙarƙashin shi, ya gaza tafiya kan hanya saboda rashin tabbas da kyaun hanya?"
"Daga Sokoto zuwa Gusau, babban birnin Zamfara tafiya ce ta tsawon kilomita 206. Jagora wanda al'ummarsa ne a zuciyarsa kuma wanda ke da tabbas ɗin tsaro ya gaza tafiya a mota."

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin mu take yi don tabbatar da zaman lafiya ya dawo Zamfara cikin ƙanƙanin lokaci, Buhari

"Kamata ya yi shugaba Buhari ya ƙara wa yan Najeriya ƙarfin guiwa ta hanyar zuwa Gusau, amma maimakom haka sai tura sakon bidiyo ga jam'ar Zamfara cewa ya ƙagu komai ya dai-daita ya samu zuwa gare su."

Soke zuwa Zamfara saɓa alkawari ne - PDP

Jam'iyyar PDP ta ƙara da cewa fasa zuwa Zamfara da Buhari ya yi wata babbar alama ce dake nuna saɓa alƙawarin da ya yi wa yan Najeriya cewa shi ne a gaba wajen yaƙar ta'addanci.

Wannan ya tabbatar da gazawar shugaban Buhari da gwamnatinsa ta APC, kuma ya tabbatar da halin da ƙasar ke ciki na ƙaƙanikayi, inji PDP.

A wani labarin na daban kuma Ɗan kwamishiniyar mata da harkokin walwala a Kano, Dakta Zahara'u ya ɓata babu wanda yasan inda yake

Rahoto daga Kano ya nuna cewa ɗan kwamishiniyar mata da walwalar al'ummar, Dakta Zahara'u Muhammad Umar, ya bata ba'a san inda yake ba.

Kara karanta wannan

Zan murƙushe yan ta'adda baki ɗaya kafin na sauka daga mulki, Shugaba Buhari

Rahoto ya bayyana cewa Abdurrahman Abdu Usman, ya bar gida da nufin zuwa Katsina, inda yake bautar ƙasa da aka fi sani da NYSC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel