Kano: Rayuka 5 sun salwanta sakamakon hatsari, FRSC ta danganta hakan da tukin ganganci

Kano: Rayuka 5 sun salwanta sakamakon hatsari, FRSC ta danganta hakan da tukin ganganci

  • Rayuka 5 sun salwantar sakamakon mugun hatsarin da mota kirar Sharon da watamota kirar Hummer suka gwabza a garin Dambatta
  • Tuni jami'an hukumar kwana-kwana da ke kusa su ne suka ceci sauran mutane 17 da basu rasu ba inda aka mika su asibiti
  • Hukuma kiyaye hadurran kan tituna ta tarayya ta alakanta hatsarin da mugun gudun da masu ababen hawan ke yi

Kano - Mutane 5 sun rasa rayukan su a sanadiyyar mummunan hatsari ababen hawa a kan titin anguwar Gamji a karamar hukumar Dambatta da ke Jihar Kano, Punch ta ruwaito.

Kakakin hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ne ya tabbatar da hatsarin, yayin da ya alakanta hakan da tukin ganganci, wanda ya janyo karo tsakanin Sharon da bus kirar Hummer.

Kano: Rayuka 5 sun salwanta sakamakon hatsari, FRSC ta danganta hakan da tukin ganganci
Kano: Rayuka 5 sun salwanta sakamakon hatsari, FRSC ta danganta hakan da tukin ganganci. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Ya ce fasinjoji 22 ne suka tafka hatsarin. Kakakin ya bayyana yadda 'yan kwana-kwana da 'yan sanda suka ceto wasu daga cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su, kamar yadda wuta ta kama Sharon din, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Ya bayyana yadda wasu jami'an kiwon lafiya suka tabbatar da mutuwar fasinjoji 5, yayin da sauran 17 suke Asibitin kwararru na Gaya inda suke samun kulawa.

Mai magana da yawun hukumar ya bayyana sunayen wadanda hatsarin ya lashe rayukan su kamar haka; Bello Muhammad, Musa Abdulqadir, Abdulaziz Bello, Halifa Muhammad da Musa Muntari.

A wani labarin mai kama da haka, wani yaro dan shekara 3, Aliyu Lawan, ya nitse a rijiya a anguwar dan Mako da ke karamar hukumar Dambatta a jihar.

"Hadakan masu ceton rai daga hukamar kashe wuta na Dambatta sun ciro gawar yayin da suka mika sa ga mahaifin sa, Malam Lawan," inji Kakakin.

Abdullahi ya bukaci mutane su zama masu lura kuma su gina rijiyoyi masu rufi mai karfi dan gudun al'amarin ya sake maimaita kansa.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

Mutane 16 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi, Hukumar FRSC

A wani labari na daban, babban kwamandan Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC, a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce a kalla mutane 16 ne suka rasu a hatsarin mota da ya faru a jihar a ranar Lahadi.

Mr Abdullahi ya tabbatar da hakan ne cikin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai ta kasa, NAN, a ranar Litinin a Bauchi, Premium Times ta ruwaito.

A cewarsa, hatsarin, wanda ya ritsa da babban mota da motar haya ta Toyota Hummer bus, ya faru ne a kauyen Bambal a hanyar Kano zuwa Jama'are misalin karfe 7 na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel