An tafka asarar miiliyoyi: Gobara ta yi kaca-kaca da shahararriyar kasuwar Neja
- An tafka asarar miiliyoyi yayin da gobara ta tashi a babbar kasuwar Mokwa da ke hedkwatar karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja
- Sarkin yankin, Ndalile-Mokwa, Alhaji Mohammed Shaba ya bayyana cewa gobarar ta lakume fiye da rabin kasuwar
- Ya ce hukumar kashe gobara sun yi iya bakin kokarinsu don kashe wutar amma abun bai zo da sauki ba saboda rashin tankuna
Niger - Gobara ta lakume kayayyaki musamman na masarufi na miliyoyin naira a babbar kasuwar Mokwa da ke hedkwatar karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja.
Daily Trust ta rahoto cewa a kalla mutane hudu musamman yan kasuwa da ke kwana a shagunansu ne suka ji munanan raunuka, an kuma kwashe su zuwa babban asibitin Mokwa domin samun kulawar likitoci.
Babban sarkin garin, Ndalile-Mokwa, Alhaji Mohammed Shaba ya fada ma Daily Trust cewa gobarar wacce ta fara da misalin karfe 4:00 na asuba ta kona fiye da rabin kasuwar kurmus.
Ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gobarar ta fara da misalin karfe 4:00 na asuba. Yayin da suka kira ni game da lamarin, nan take na kira hukumar kashe gobara. Sun yi kokarin kashe wutar amma saboda rashin tankuna, abun bai zo da sauki ba."
Ya ce wasu bata gari sun yi amfani da wannan damar wajen sace kayayyaki amma an kama hudu daga cikinsu.
Ya ce:
"Wannan kasuwa ce ta karkara inda ake siyar da kayayyakin abinci da yawa. Kuma mun kasance gada tsakanin arewa da kudu ta bangaren kai kayayyakin abinci. Fiye da rabin kasuwar ta kone."
Daya daga cikin yan kasuwar wanda aka bayyana a matsayin Etsu-Kpo Mokwa ya ce yan kasuwa na ta harhada yawan asarar da suka yi, inda ya bayyana lamarin a matsayin gagarumin barna.
Ya ce:
"Yan kasuwa da dama za su shafe shekaru masu yawa kafin su farfado daga wannan annoba. Har yanzu muna kirga asarar da muka yi. Jami'an hukumar kashe gobara na nan suna iya bakin kokarinsu don kashe wutar."
Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni
A wani labari makamancin wannan, wata gagarumar gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Gamboru Ngala a jihar Borno, lamarin da yasa daruruwan 'yan gudun hijiran suka rasa matsuguni.
Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya auku da yammacin Lahadi inda gobarar ta lamushe wurare masu tarin yawa a sansanin.
Wani jami'in hukumar taimakon gaggawa ta jihar, SEMA, da ke Gamboru Ngala, Malam Yusuf Gulumba, ya sanar da Daily Trust cewa an fara binciken abinda ya kawo gobarar.
Asali: Legit.ng