Da duminsa: Yan takara 7 a zaben fidda gwanin APC sun janye, sunce Gwamnan murdiya ya shirya

Da duminsa: Yan takara 7 a zaben fidda gwanin APC sun janye, sunce Gwamnan murdiya ya shirya

  • Kamar yadda aka yi a na PDP jiya, an fara zanga-zanga kan zaben fidda gwanin jam'yyar APC a Ekiti
  • Yan takara bakwai sun yi kira ga uwar jam'iyya ta dage zaben daga yau saboda idan akayi za'ayi magudi
  • Sun ce gaba daya a canza mambobin kwamitin zaben saboda sun gano yaran gwamnan ne

Ekiti - Yan takaran kujeran gwamnan jihar Ekiti guda bakwai sun janye daga zaben fidda gwanin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta shirya yau a jihar.

Yan takaran sune; Kayode Mojo, Demola Popoola, Femi Bamisile, Bamidele Faparusi, Dayo Adeyeye, Opeyemi Bamidele da Afolabi Oluwasola.

Sun yi zargin cewa kwamitin zabe cike take da yaran Gwamnan jihar, Kayode Fayemi, rahoton Thecable.

Sun kara da cewa Gwamnan na kokarin kakaba musu, Biodun Oyebanji, matsayin wanda zai wakilci jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan Hanifa, an sake kashe wata yarinya a jihar Kano: Gwamna Ganduje

Gwamnan murdiya ya shirya
Da duminsa: Yan takara 7 a zaben fidda gwanin APC sun janye, sunce Gwamnan murdiya ya shirya Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da suka saki ranar Alhamis, sun bayyana cewa babu yadda za'a yi adalci a zaben saboda irin mutanen dake kwamitin zabe.

Jawabin yace:

"Yan takara bakwai sun yi mamakin ganin jerin sunayen mambobin kwamitin na kananan hukumomi na unguwanni duk mambobin jam'iyya ne da masu rike da mukaman siyasa da Gwamna ya basu kuma sun dade suna goyon bayan dan takara Biodun Oyebanji, tsohon sakataren gwamnatin jihar."
"Kowa ya sani cewa Gwamnan Kayode Fayemi ya bayyana goyon bayansa ga Biodun Oyebanji."
"Abin bakin cikin shine daga ganin jerin sunayen mambobin kwamitin zaben, za ka ga duk masu rike da mukaman gwamnati ne kuma magoya bayan wani dan takara a zaben."

Yan takaran sun yi kira ga jam'iyyar ta canza mambobin kwamitin zaben a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel