Gwamnatin Kano ta bada umurnin rufe makarantar da aka kashe Hanifa Abubakar

Gwamnatin Kano ta bada umurnin rufe makarantar da aka kashe Hanifa Abubakar

  • Gwamnatin Kano tayi maganarta ta farko bayan labarin kisan dalibar makaranta da shugaban makaranta ya kashe
  • Hukumar yan sandan ta tabbatar da damke shugaban makarantar da ya sace Hanifa Abubakar kuma ya kasheta
  • An sace Hanifa, Yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano a hanyarta ta dawowa daga Islamiyya kwanaki 46 da suka gabata

Gwamnatin jihar Kano ta bada umurnin kulle makarantar Noble Kids Academy dake Kwanar Dakata, karamar hukumar Nasarawa, inda aka tono gawar daliba Hanifa Abubakar.

Kwamishanan ilimin jihar, Muhammad Kiru, ya sanar da hakan ne a jawabin da ya saki bayan damke shugaban makarantar, rahoton Punch.

Kiru, wanda ya bayyana alhininsa ya ce bayan kulle makarantar, gwamnatin jihar zata kaddamar da bincike kan makarantu masu zaman kansu marasa rijista da Malamai don gujewa irin wannan fitina.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa

Kabarin Hanifa Abubakar
Gwamnatin Kano ta bada umurnin rufe makarantar da aka kashe Hanifa Abubakar Hoto: SP Kiyawa
Asali: Facebook

Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano

Mammalakin makarantar Noble Kids School dake jihar Kano ya shiga komar yan sanda kan laifin garkuwa da kashe dalibar makarantarsa, Hanifa Abubakar yar shekara biyar.

Yan'uwanta sun bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka je gidan iyayenta jajanta musu lokacin da aka sace ta.

Hukumar yan sanda a Kano ta tabbatar da damke Malamin, Abdulmalik Tanko, wanda yayi garkuwa da ita.

Kakakin yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis.

Yace bayan dogon bincike da bibiya, jami'an DSS sun damke Abdulmalik Mohammed Tanko da Hashim Isyaku, yan unguwar Tudun Murtala Quarters, karamar hukumar Nassarawa.

Yayin bincike, AbdulMalik ya amsa cewa Hanifa dalibarsa ce a makaranta kuma ya saceta kuma ya kasheta bayan ta ganeshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel