Gwamnan Arewa ya ɗau Zafi, yace zai rattaba hannu kan dokar kashe duk mai hannu a ta'addancin yan bindiga

Gwamnan Arewa ya ɗau Zafi, yace zai rattaba hannu kan dokar kashe duk mai hannu a ta'addancin yan bindiga

  • Gwamnan jihar Filato, yace ko shakka ba zai yi ba wajen rattaba hannu kan dokar da zata yanke hukuncin kisa ga masu ta'addanci a jiharsa
  • Lalong ya yaba da matakan da jami'an tsaro ke ɗauka musamman idan suka samu rahoton yunkurin sace mazauna jihar
  • Yace duk da haka hukumomin tsaro na bukatar taimakon mutane da bayanai domin kawo karshen lamarin baki ɗaya

Platea - Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace ba zai yi wata-wata ba wajen rattaba hannu kan dokar da zata yanke wa duk mai hannu a garkuwa da mutane hukuncin kisa.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wata sanarwa da darakatan watsa labaransa, Macham Makut, ya fitar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Lalong ya bayyana cewa ayyukan yan bindiga da sace mutane a jihar na neman wuce gona da iri, gwamnati ba zata rike hannu tana kallo ba.

Kara karanta wannan

Babbar magan: Gwamna ya sanya hannu ya doka mai tsauri ta hana kiwo a fili

Gwamna Lalong na jihar Filato
Gwamnan Arewa ya ɗau Zafi, yace zai rattaba hannu kan dokar kashe duk mai hannu a ta'addancin yan bindiga Hoto: @LalongBako
Asali: Twitter

Gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba zan yi shakkar rattaba hannu kan dokar yanke hukuncin kisa ga duk wanda doka ta tabbatar da yana da hannu a garkuwa da mutane ba. Tun shekarar da ta gabata muka sa hannu kan dokar garkuwa, a shirye muke mu aiwatar da ita."

Lalong ya yaba da nasarorin hukumomin tsaro

Gwamnan ya kuma yaba da matakan da hukumomin tsaro suke cigaba da ɗauka game da masu garkuwa da mutane a faɗin jihar.

Ya yi misali da ceto Basaraken masarautar Vwang, Da Gyang Gutt Balak, da kuma damƙe waɗan da ake zargi, inda yace wannan cigaba ne mai kyau da ya kamata jami'ai su ɗora a kai.

Lalong yace jami'an tsaro sun sake samun irin wannan nasara lokacin da yan bindiga suka sace ɗalibai a kwalejin fasaha dake Barkin Ladi, inda aka ceto su jim kaɗan bayan sace su.

Kara karanta wannan

Abin da yasa Gwamnatin Tarayya ba za ta dena karɓo rancen kuɗi ba, Lawan

Wani sashin sanarwan yace:

"Gwamna Lalong ya yaba wa jami'an tsaro bisa matakan da suke ɗauka kan yan bindigan dake sace mutane, wanda ya jefa tsoro a zuƙatan mutane."
"Lalong ya nuna jin daɗinsa kan yadda jami'an tsaro ke ɗaukar mataki nan take da zaran sun musu kiran gaggawa game da sace mazauna jihar mu, wanda hakan ke sa su kwato mutanen."

Me ya kamata mutane su yi don taimaka wa tsaro?

Gwamnan ya yi kira ga mazauna jihar su taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan sirri da zasu taimaka musu wajen ɗaukar mataki.

A cewarsa, goyon bayan al'umma ne kaɗai zai sa hukumomin tsaro su iya kawo ƙarshen ta'addancin yan bindiga, waɗanda ke tada hankulan mutane.

A wani labarin na daban kuma Yan sanda sun yi magana kan wurin da Bello Turji ya koma bayan tserewa daga Zamfara

Rundunar yan sanda ta jihar Kwara ta musanta ikirarin ɗan majlisar wakilan tarayya game da gawurtaccen ɗan bindiga, Bello Turji.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matawalle ya ce suna shirin tona asirin masu aiki tare da ƴan ta'adda

Ɗan majalisar ya bayyana cewa luguden wutan sojojin Najeriya ya sa Turji ya tsere daga Zamfara, ya kafa sansani a dajin Kwara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel