Wani matashi ya mutu yayinda yake kokarin satar wayoyin Taransfoma

Wani matashi ya mutu yayinda yake kokarin satar wayoyin Taransfoma

  • Wani mutumi ya gamu da ajalinsa a jihar Kano yayinda ya shiga gidan Taransfoma satan wayoyi
  • Mutan unguwan sun bayyana yadda suka ji iwun mutumin cikin dare da tashin wayoyi
  • Wannan ba shi ne karo na farko da barayin kayan wuta ke mutuwa lokacin satan ba

Jihar Kano - Wani matashi ya rasa rayuwarsa a garin Lambu, karamar hukumar Tofa ta jihar Kano yayinda yake kokarin sace wayoyin dake jikin Taransfoma.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne misalin karfe 1 na daren Laraba.

Wani mazaunin garin, Naziru Lambu, ya bayyanawa manema labarai cewa mutumin ya samu nasarar sace wasu daga cikin wayoyin kuma ya ajiye kusa da Taransfoman.

Yace Makwabta sun bayyana yadda suka ji karar tashin wayoyi cikin dare da kuma iwun mutumin kafin ya mutu.

Wani matashi ya mutu yayinda yake kokarin satar wayoyin Taransfoma
Wani matashi ya mutu yayinda yake kokarin satar wayoyin Taransfoma
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Naziru ya kara da cewa an ga gawarsa kan Taransfoman tare da wayar hannu da layuka.

Jami'an hukumar Sibil defens, yan sanda da ma'aikatan kamfanin lantarkin KEDCO sun dira Lambu don ganin abinda ya faru, ya kara.

Haka ya faru a jihar Delta

Irin wannan abu ya faru kwanakin baya inda aka ga bidiyon wani matashi da ake zargin mai satan kayayyakin wutan na na'uran taransfoma ya gamu da ajalinsa yayinda aka tsinci gawarsa cikin na'urar a yau.

Bidiyon wanda ya nuna mutane a bakin titi suna kallon ikon Allah suna baiwa juna labarin abinda ya faru.

Wanda ya daura nidiyon a shafin Facebook ya bayyana cewa wannan abu ya faru ne a garin Asaba, babbar birnin jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel