Gwanda mu mutu da yan wasan Super Eagles su kayar da mu yau, Guinea Bissau

Gwanda mu mutu da yan wasan Super Eagles su kayar da mu yau, Guinea Bissau

  • Yayinda ake shirin fafatawa tsakanin Najeriya da Guinea Bissau yau, yan kwallon sun ce sai dai a mutu
  • Najeriya tuni ta haye matakin kifa daya kwala bayan lashe wasanninta biyu na farko inda ta lallasa Misra da Sudan
  • A wasan yau, kocin Super Eagles ya ce sabbin yan wasa zai zuba don baiwa wasu daman taka leda

Kyaftin na yan kwallon kasar Guinea Bissau, Jonas Azevedo Mendes, ya lashi takobin cewa gwamma su mutu yau da yan kwallon Najeriya, Super Eagles, su kayar da su a wasan yau.

Mendes ya bayyana cewa zasu fafata da yan Najeriya da dukkan karfin da suke da shi kuma zasu tabbatar da cewa basu tafi gida ba.

Najeriya za ta kara da Guinea Bissau yau Laraba misalin karfe 8 na dare a wasa na uku na gasar kasashen nahiyar Afrika dake gudana a kasar Kamaru.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

Guinea Bissau
Gwanda mu mutu da yan wasan Super Eagles su kayar da mu yau, Guinea Bissau Hoto
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayinda aka tambayesa shin akwai wani dan kwallon Najeriyan da suke shirin ganin sun dakile, yace:

"Mun san Najeriya na da yan kwallo masu kyau. Kuskure ne muce zamu dakile mutum guda. Zamu fuskancensu gaba daya."

Guinea Bissau, wacce ke tare da Najeriya, Misra da Sudan ta sha kaye hannun Misra kuma tayi kunnen jaki da Sudan.

Idan ta samu nasara kan Najeriya yau, zata haye matakin kifa daya kwala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel