Kotu Ta Sake Ba Hukumar INEC Umarni kan Saka Sunan Ɗan Takarar Gwamnan PDP

Kotu Ta Sake Ba Hukumar INEC Umarni kan Saka Sunan Ɗan Takarar Gwamnan PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci INEC ta amince da Oladipupo Adebutu a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Ogun
  • Mai shari’a Peter Lifu ya ba INEC umarnin wallafa sunan Adebutu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a cikin sa’o’i 24
  • Kotun ta bayyana cewa INEC ba ta da ikon cire sunan ɗan takarar da jam’iyya ta tsayar bisa ƙa’ida ba tare da izinin kotu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta amince da dan takarar gwamna a Ogun.

Kotun ta bukaci INEC ta dawo da sunan Oladipupo Adebutu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Ogun na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Kotu ta tsige ɗan takara a jam'iyyar su Kwankwaso ana shirin zaben 2027

Mai shari’a Peter Lifu ne ya bayar da wannan umarni a hukuncin da ya yanke ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamban 2026, cewar Punch.

Alkalin ya umarci INEC da ta wallafa sunan Adebutu a matsayin ɗan takarar da PDP ta tsayar a hukumance cikin sa’o’i 24.

Kotun ta bayyana matsayin INEC

Mai shari’a Lifu ya bayyana cewa INEC ba ta da ikon cire sunan ɗan takarar da wata jam’iyya ta tsayar bisa ƙa’ida da kanta.

Ya ce matakin da hukumar zaɓen ta ɗauka ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, doka da kuma ƙa’idojin da suka shafi zaɓe.

Alkalin ya ƙara da cewa kotu ce kaɗai ke da ikon ayyana cewa ɗan takarar jam’iyya bai cancanta ba, ba INEC ba.

An tauye wa Adebutu haƙƙinsa

Haka kuma, kotun ta bayyana cewa INEC ta tauye wa Adebutu haƙƙinsa na samun shari’a ta adalci (fair hearing).

Hukuncin ya zo ne yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan Ogun na shekarar 2027 wanda ake ci gaba da rikici kan tikitin.

The Nation ta wallafa rahoton cewa kotun ta ba INEC wa’adin sa’o’i 24 domin aiwatar da umarnin.

Ƙarin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.