Yadda zuwan Osinbajo Kano ta’aziyya da shiga masallaci da takalmi ya bar baya da kura

Yadda zuwan Osinbajo Kano ta’aziyya da shiga masallaci da takalmi ya bar baya da kura

  • Mataimakin shugaban Najeriya ya kai ziyara zuwa jihar Kano domin ta’aziyya da laccar Sardauna
  • Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ta’aziyya a gidan Bashir Tofa da masallacin Ahmad Ibrahim Bamba
  • Osinbajo ya shiga masallacin unguwar Tudun Yola da takalminsa wajen yi wa malamai ta’aziyya

Kano - A ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya na jihar Kano, inda ya gabatar da wata lacca da aka shirya.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana Marigayi Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello a matsayin shugaban da ba za a manta da irin ayyukan alherin shi ba.

Sardauna Memorial Foundation ta shirya wannan zaman mai taken farfado da masarautun gargaji wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa.

“Yadda ya kaunaci talakawa, saukin ransa, da alherin da ya yi abin a yaba ne. Yadda aka tsara masarautun gargajiya a Arewa, aikin Sardaunan Sokoto ne.”

Kara karanta wannan

Bayan mutuwarsa, wani mutumi ya bada labarin alherin da Bashir Tofa ya yi masa a 1991

- Yemi Osinbajo

Ta'aziyya

Baya ga haka, Mai girma Farfesa Osinbajo ya je ya yi ta’aziyya ga iyalin Marigayi Bashir Othman Tofa da wani Alhaji Hasan wadanda suka rasu a watan nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook, mataimakin shugaban kasar ya na masallacin Tudun Yola inda ya yi ta’aziyyar rashin Dr. Ahmad I. Bamba.

Osinbajo a Kano
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: professoryemiosinbajo
Asali: Facebook

An shiga masallaci da takalmi

Sai dai an ga Osinbajo yana sanye da takalmi a cikin masallacin yayin da ya zo yin ta’aziyyar. Hakan ya jawo wasu suke ta maganganu a shafin Facebook.

Legit.ng Hausa ta bibiyi shafin Malam Ibrahim El-Caleel, wanda ya ba Osinbajo uzuri, ya ce na-kusa da shi ne ba su fada masa cewa ya cire takalamin na sa ba.

“Musulmai sukan yi nauyin baki wajen faɗawa waɗanda ba musulmai ba cewa abu kaza ba daidai bane. Da an ce da Osinbajo ya cire takalmin shi, zai cire dole. Tun da shine yake son yin ta’ziyyah..."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya su rika yi mana adalci kan lamarin tsaro, muna kokari:Shugaba Buhari

"Amma a nan ni ban ga lefin Osibanjo ba. Don kuwa ba dole bane ya halarto cewa abinda yayi bai kyauta ba. A matsayin shi na ɗan siyasan dimukraɗiyyah, bana tunanin da gangan zai yi wannan aikin da yayi don cin fuska.” - El-Caleel

An yi kuskure dai...

Shi kuma Adnan Muktar Tudun-Wada ya ce ya yi bakin-ciki, kuma an yi kuskure da aka bar Osinbajo da takalmansa, ya kuma soki masu neman ba abin kariya.

"Maganar gaskiya da Osinbajo ya cire takalmin sa tun da mu ma musulmai idan zamu shiga masallaci cirewa muke. Wadanda basu nusar dashi hakan ba sune suka kwafsa. Kuskure an riga anyi, fatan mu a gyara anan gaba. Shikenan fa.”

- Adnan Mukhtar Tudunwada

Wasu kuma su na ganin akwai burbushin siyasa a wannan ziyara domin a baya mutane da-dama sun mutu, amma Osinbajo bai zo ta’aziyya a jihar Kano ba.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara

"Jiya Tinubu ya zo. Yau Osinbajo ma ya zo. Dama Kanon “Ka zo na zo” ce. A cigaba kawai."

- Ahmad Abacha

Asali: Legit.ng

Online view pixel