Yanzu-Yanzu: Ɗan Siyasar Najeriya Na Jamhuriya Ta Biyu, Guy Ikokwu, Ya Rasu

Yanzu-Yanzu: Ɗan Siyasar Najeriya Na Jamhuriya Ta Biyu, Guy Ikokwu, Ya Rasu

  • Cif Omenife Guy Ike Ikokwu, gogaggen dan siyasar Najeriya na Jamhuriya ta biyu ya riga mu gidan gaskiya
  • Guy Ikokwu ya rasu yana da shekaru 85 kamar yadda sanarwar da iyalansa suka fitar ta bayyana
  • Cif Ikokwu ne shugaban Jam'iyyar, NPP, a tsohuwar Jihar Anambra, kuma shine shugaban PDP, na farko a Anambra

Dan siyasar Najeriya, Cif Guy Ikokwu, ya riga mu gidan gaskiya.

Ya rasu ne yana da shekaru 85 a duniya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: Ɗan Siyasa Na Jamhuriya Ta Biyu, Guy Ikokwu, Ya Rasu Yana Da Shekaru 85
'Dan Siyasa Na Jamhuriya Ta Biyu, Guy Ikokwu, Ya Rasu. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shugaban iyalan Ikokwu, Cif Ugonna Ikokwu, ya tabbatar da rasuwar dan siyasar cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

Sanarwar ta ce:

"A madadin Cif Ugonna Ikokwu, Shugaban iyalan Ikokwu na Oba, ina sanar da rasuwar Chief Omenife Guy Ike Ikokwu, tsohon shugaban Otu Oka-Iwu, a ranar Laraba 12 ga watan Janairun 2022. Shekarunsa 85.

Kara karanta wannan

Hotunan Buhari yayin da ya ziyarci iyalan Marigayi Shonekan don yi masu ta’aziyya

"Ya rasu ya bar 'ya'ya 4 da jikoki, kanai da yayi 7 sannan 'yan uwa da dangi masu yawa.
"Iyalansa za su bada karin bayani a nan gaba.
"A halin yanzu, muna cigaba da rokon addu'a daga gare su domin Allah ya jikan ran Omenife ya saka masa da aljanna."

Ikokwu ne shugaban Jam'iyyar Nigerian Peoples Party, NPP, a tsohuwar Jihar Anambra, kuma shine shugaban Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na farko a Anambra.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel