Boko Haram sun shiga jami’ar sojoji, sun fatattaki dakarun Najeriya daga Makarantar Sojoji dake Buratai

Boko Haram sun shiga jami’ar sojoji, sun fatattaki dakarun Najeriya daga Makarantar Sojoji dake Buratai

  • Sojojin Islamic State in West Africa Province (ISWAP) sun shiga har cikin jami’ar Biu a jihar Borno
  • Wannan ne karo na biyu da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai hari a karamar hukumar Biu a makon nan
  • A lokacin da Janar Tukur Yusufu Buratai yake hafsun soja ne aka gina jami’ar sojoji a jihar Borno

Borno - Dakarun ISWAP sun fitar da bidiyon mayakansu su na kai hari a jami’ar sojoji da ke kauyen Buratai, Biu, jihar Borno.

Mayakan na ISWAP sun shiga sashen koyon ilmin yaki na Tukur Yusufu Buratai Institute for War and Peace (TBI) da ke cikin jami’ar sojoji da ke garin Biu.

Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai harin ne a karshen makon nan.

A bidiyon za a ga ‘yan ta’addan su na ta harbe-harbe ba tare da sojoji sun kawo masu martani daga sojoji. Za a iya ganin motocin sojoji a ajiye babu kowa.

Kara karanta wannan

Rudani: 'Yan Boko Haram sun sace malaman makarantar 'yan sanda a Borno

Gajeren bidiyo

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta gani a bidiyon da aka fitar, ‘yan ta’addan na Boko Haram sun rika kona tutocin sojojin kasa da na Najeriya, su na yin kabarbari.

Boko Haram
Jami'ar sojoji ta Biu Hoto: NAUniBiu
Asali: Facebook

Wasu ‘yan ta’addan na kungiyar ISWAP sun shigo jami’ar su na ta harbe-harbe, yayin da za a iya hangen wasu mayakan a cikin motocin da sojoji ke aiki da su.

Da suka zo inda aka ajiye motocin jami’an sojoji, ‘yan ta’addan sun sauko da tutoci kasa, sun kona su. Za a iya ganin ‘yan ta’addan su na bankawa tutocin wuta.

Wannan shi ne hari na biyu da ‘Yan Boko Haram suka kai garin Buratai a makon nan. A ranar Litinin an kai hari aka fatattaki mazauna yankin, su ka tsere.

IReporteronline sun tabbatar da labarin wannan labarin a ranar Juma'a, 14 ga watan Junairu, 2022.

Kara karanta wannan

Magoya baya sun ba Sanatan APC kwana 90 ya ayyana niyyar takarar Gwamna ko su je kotu

Jami'ar sojoji a kauyen Buratai

An gina jami’ar sojojin da ke garin na Biu a Borno ne a lokacin da Laftanan-Janar Tukur Yusuf Buratai yake rike da kujerar shugaban hafsun sojojin kasa.

A halin yanzu Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) shi ne Jakadan Najeriya zuwa kasar Benin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel