'Yar Shugaban kasa, Zahra Buhari, ta yi magana kan meyasa ba'a son Maza na kuka

'Yar Shugaban kasa, Zahra Buhari, ta yi magana kan meyasa ba'a son Maza na kuka

  • Diyar Shugaban kasa ta yi bayani yadda take mamakin dalilin da yasa ba'a son ganin maza na kuka
  • A cewarta, zuciyar mace daya ne da namiji saboda haka ya kamata maza su rika kuka
  • Yan Najeriya a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun yi martani kan wannan maganar da tayi

Zahra Buhari-Indimi, 'diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa tana mamakin dalilin da yasa ba a son ganin maza suna kuka duk da su ma yan Adam ne kaman matan.

A tsokacin da tayi a shafinta na Instagram, Zahra ta yi addu'an Idan Allah ya yarda a AlJannah ba za muyi kuka ba.

A hoton da ta daura dauke da rubutun larabci da turanci mai cewa 'A Aljannah, ba zamu taba kuka ba'.

A kasa sai ta kara da jawabin cewa:

Kara karanta wannan

Watanni bayan mutuwar wani Mufti, Kyanwarsa taki tashi daga kan kabarinsa

"Wani lokaci sai kayi mamakin me yasa ba'a son ganin maza na kuka?....Idan mace na jin shauki, shi ma namiji yana ji."

'Yar Shugaban kasa, Zahra Buhar
'Yar Shugaban kasa, Zahra Buhari, ta yi magana kan meyasa ba'a son Maza na kuka Hoto: @mrs_zmbi
Asali: Instagram

Martanin yan Najeriya

Nura C Ibrahim:

Allah sarki saboda idan maza sukayi kuka lamari ya baci sune suke rarrashin mata kuma sannan aga suna kuka

Aliyu Santuraki Yunusa:

Kitambayi babanki lokutan dasha Kaye azabe miyasashi kuka

Mohammed Husaini JB:

In namiji daya yayi kuka sai mata goma sunyi

Sheikh Ahmad Sadees:

Ki tambayi lusarin babanki Danliti mugu

Idris Musa Nyabo:

Shiyasa mai dattin hula ya yaudaremu da kuka kenan?

Sulaiman Azare:

A madadin Baba manjo daya Jagoranci tawagar ƙare kukan maza a 2015 ke kuma kikeson sai an cigaba muna Allah wadai da wannan yunƙuri naki.

Yakub Chamba Sani:

2011 da ubanki yaji kayi baiyi ba saboda kunshiga daula kun manta ko,

Asali: Legit.ng

Online view pixel