Asiri ya Tonu: An kama wata mata da ta yi yunkurin siyar da ɗan kishiyarta a Zamfara

Asiri ya Tonu: An kama wata mata da ta yi yunkurin siyar da ɗan kishiyarta a Zamfara

  • Wata mata, Aisha Ibrahim, ta shiga hannun jami'an yan sanda bisa zargin sace ɗan kishiya da yunkurin siyar da shi
  • Kwamishinan yan sanda reshen jihar Zamfara, Ayuba Elkana, yace matar yar asalin wani kauye ne a Jamhuriyar Nijar
  • Matar tace ta ɗauki matakin siyar da yaron ɗan shekara biyu ne domin rama abinda kishiyar ta mata a baya

Zamfara - Hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara ta kama wata mata, Aisha Ibrahim, da ta yi yunkurin siyar da yaro ɗan shekara biyu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa yaron da matar ta yi kokarin siyarwa ya kasance ɗa ga kishiyarta.

Da yake jawabi ga manema labara a Gusau, ranar Alhamis, kwamishinan yan sanda, Ayuba Elkana, yace yan sanda sun kama matar ne ranar 8 ga watan Janairu, a yankin Tullukawa, ƙaramar hukumar Gusau.

Kara karanta wannan

Bayan sanar da Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zai gogayya da Tinubu a 2023

Yan sanda
Asiri ya Tonu: An kama wata mata da ta yi yunkurin siyar da ɗan kishiyarta a Zamfara Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Kwamishinan yan sanda na Zamfara yace:

"Matar da ake zargin yar asalin ƙauye Danyade Kaya dake karamar hukumar Maraɗi a Jamhuriyar Nijar ce, ta shiga hannu ne ɗauke da ɗan kishiyarta."
"Kuma matar ta amince da aikata laifin sato ɗan kishiyarta, domin ɗaukar fansar abinda kishiyar ta mata na sace ɗanta kuma ta siyar."
"Matar ta kuma ƙara da bayyana cewa dalilin sace yaron shi ne domin ta siyar da shi, ta samu kudin kashewa na yau da kullum."

Wane mataki yan sanda zasu ɗauka?

Kwamishinan yan sandan yace hukumarsa zata miƙa matar ga hukumar shige da fice ta ƙasa domin ɗaukar matakin da ya dace, kamar yadda BBC Hausa ta rahoto.

Elkana ya kuma yi kira ga al'umma su fahimci kokarin da hukumomin tsaro ke yi ba dare ba rana wajen dakile aikata manyan laifuka a jihar.

Kara karanta wannan

Atiku ya aike da muhimmin sako ga hukumomin tsaro kan kisan mutum 200 a Zamfara

Kazalika ya kuma roki mazauna jihar Zamfara su cigaba da addu'a domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun yi mummunar ɓarna a babbar Sakateriyar jam'iyyar PDP

Wasu yan bindiga ɗauke da muggan makamai da ake zargin yan daban siyasa ne sun farmaki sakatariyar PDP reshen jihar Ekiti.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi raga-raga da kujeru, sun lalata fayil-fayin, sannan kuma suka farfasq gilasan kofofi da tagogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel