Baturiya ta kashewa saurayinta makudan kudi, tana shirin zuwa Najeriya aurensa

Baturiya ta kashewa saurayinta makudan kudi, tana shirin zuwa Najeriya aurensa

  • Wata baturiya ta shirya auren matashi dan Najeriya wanda ta fada runbun soyayya da shi
  • Baturiyar yar shekara 60 ta hadu da dan Najeriya mai shekaru 22 a kafar ra'ayi da sada zumunta kuma tana matukar son sa
  • A cewarta, bai tambayanta kudi kuma kawo yanzu ta kashe masa $4500 (N1.8million) kan saurayin

Wata baturiya yar shekara 60 ta bayyana dan Najeriya, Peter, dan shekaru 22 a matsayin masoyin da bata taba haduwa da mai son ta irinsa ba tun lokacin da ta fara soyayya a rayuwarta.

Matar ta bayyana hakan ne a shirin Dr. Phil Show.

Yadda suka hadu

Matar ta bayyana yadda suka hadu a kafar ra'ayi da sada zumunta.

A cewarta, ta yi magana ne a wani shafi kuma Peter ya yi tsokaci saga baya kuma ya tura mata sako.

Kara karanta wannan

Angon Instagram: Yadda budurwa ta cire kunya tayi abin da ya dace, ta yi wuf da matashi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka suka fara abota na tsawon watanni kuma abotar ta rikide zuwa soyayya.

Baturiya ta kashewa saurayinta makudan kudi, tana shirin zuwa Najeriya aurensa
Baturiya ta kashewa saurayinta makudan kudi, tana shirin zuwa Najeriya aurensa Hoto: Dr Phil
Asali: Facebook

Bai tambayarta kudi

Tsohuwar, yayinda amsa tambayoyi kan shin bata ji tsoron ko dan damfara bane, tace Peter ba taba tambayarta kudi ba tun lokacin da suka hadu.

Tace da ya taba haka, da zargin da yan'uwanta ke yi ya tabbata cewa dan damfara ne.

Tace da kanta ta bashi kudi yayi fasfot, ya sayi waya kuma ya kama gida. Tace ta kashe $4500 (N1.8million) kansa kuma zata shigo Najeriya aurensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel