Abin da ya sa matsalar tsaro ke neman gagarar hukuma - Hamza Al-Mustapha ya fadi sirrin

Abin da ya sa matsalar tsaro ke neman gagarar hukuma - Hamza Al-Mustapha ya fadi sirrin

  • Manjo Hamza Al- Mustapha yace masu kudi da mala’u suke jawo ake fama da matsalar tsaro a Najeriya
  • Tsohon Dogarin na Janar Sani Abacha ya zargi Attajirai da kashe dukiyarsu domin tada tarzoma
  • Hamza Al- Mustapha ya shaidawa ‘yan jarida cewa zai yi wahala a iya yakar masu tada zaune-tsayen

Abuja - Manjo Hamza Al- Mustapha wanda ya taba zama jami’in da ke kula da tsaron Janar Sani Abacha, ya yi magana game da sha’anin rashin tsaro a Duniya.

Jaridar Vanguard ta rahoto Manjo Hamza Al- Mustapha yana zargin masu kudi da hannu a matsalar tsaron da ya addabi jihohi da dama yanzu a Najeriya.

Hamza Al-Mustapha yace attajiran da su ke iya mallakar manyan makamai da miyagun kwayoyi ne ummul-haba’isin halin da al’umma suka shiga ciki a yau.

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun gaza, Gwamnan Arewa ya sake ba Talakawa shawara su tanadi bindigogi

Da yake zantawa da manema labarai a gidan rediyon VOA, Manjo Al- Mustapha ya bayyana cewa akwai bukatar masu kishin kasa su hada-kai, su ceto Najeriya.

Tsohon sojan yace dole sai masu mulki sun tashi tsaye domin a magance matsalar da ake ciki saboda akwai wadanda ke kashe kudi domin kawo tarzoma.

Hamza Al-Mustapha
Manjo Hamzah Al Mustapha Hoto: @Mustapha Gada (Sarkin Yakin Gada)
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin Manjo Hamzah Al Mustapha

“Lokaci ya yi da duk wani mai kishin Najeriya, mai son kasar nan ko Afrika ko Duniya a ransa, ya tashi-tsaye, ya bada gudumuwarsa.
“Abubuwa ba su tafiya yadda suka kamata. Akwai mutanen da suke kashe kudinsu domin su tada zaune-tsaye, da alama su na yin nasara.”
“Yadda suke da makamai yanzu a Afrika, da kuma kwayoyi iri-iri da mutanen da suke amfani da su, sun fara neman karbe iko a kasashe.”

- Hamzah Al Mustapha

Kara karanta wannan

A kusan karon farko, rikakken ‘Dan adawa, Sule Lamido ya yabawa matakin da Buhari ya dauka

Masu hako ma'adanai su na ta'adi?

A hirarsa da VOA Hausa, tsohon dogarin na shugaba Abacha ya koka a kan yadda aka ba wasu tsiraru damar hako ma’adanai da albarkatun da ke cikin kasa.

Wadannan masu hako ma’adanai sun gagari hukuma, Al Mustapha yace duk wanda ya nemi ya taba su, za su hada-kai da kasashen waje, har sai sun ga bayansa.

Yadda ‘Yan bindiga ke barna a Zamfara

A makon nan aka ji cewa 'yan bindiga su na yin taron-dangi su yi lalata da mata da karfin tsiya a wasu kauyukan Zamfara, inda matsalar tsaro ya yi kamari sosai.

Miyagun ‘yan bindigan sun fitini yankin Tsafe, su na kwanciya da matan mutane da karfi-da yaji. Duk macen da ta nemi tayi masu gardama, za ta bakunci barzahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel