‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban ASUU da tsohon ‘Dan takarar Gwamna

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban ASUU da tsohon ‘Dan takarar Gwamna

  • Babban jigon PDP, Honarabul Kemi Nshe ya fada hannun ‘yan bindiga a karamar hukumar Shendam
  • Ana neman N50m a hannun iyalin Hon. Nshe wanda ya taba rike shugaban karamar hukumar Shendam
  • ‘Yan bindiga sun kuma yi awon-gaba da wani malamin jami’a a garin Bosso, Dr. Monday Hassan

Plateau - ‘Dan takarar gwamnan jihar Filato a zaben 2019, Kemi Nshe, ya fada hannun miyagun ‘yan bindiga, an bukaci su biya kudin fansa.

Jaridar Punch Metro ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 3 ga watan Junairu, 2021 cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Honarabul Kemi Nshe.

Kemi Nshe ya na cikin jagororin jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Filato, ya taba rike kujerar shugaban karamar hukuma a Shendam.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon dan takarar gwamna a jihar Arewa

Rahoton yace an yi garkuwa da Hon. Kemi Nshe ne tare da shugaban kungiyar ASUU na reshen jami’ar jihar Filato, Dr. Monday Hassan.

'Yan bindiga sun dauke malamin jami'a

Dr. Monday Hassan ya na koyarwa ne a jami’ar Filato da ke garin Bokkos yayin da Honarabul Kemi Nshe babban ‘dan siyasa ne a yankin.

Hassan ya na karantar da ilmin huldatayyar kasashe, ya yi digirinsa na farko da na biyu ne a jami'ar UNIJOS da ABU Zaria a 1994 da 2008.

Simon Bako Lalong
Gwamnan Filato, Simon Bako Lalong Hoto: @LalongBako
Asali: Twitter

An kuma samu labari daga shafin Linda Ikeji Blog cewa ‘yan bindigan sun hada da wasu mutane biyu sun yi gaba da su a gidan Hon. Nshe.

An hada da abokan Hon. Nshe

Ana zargin cewa ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su abokan tsohon shugaban hukumar na Shendam ne da ke kudancin jihar Filato.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kai samame sansanin ‘yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutum 9

Majiyoyi a garin Jos sun tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun yi gaba da wadannan Bayin Allah, kuma har yanzu babu labarin inda suka shiga.

Nshe ya fito ne daga yanki daya da Mai girma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong.

‘Yanuwan Nshe sun ce cikin dare aka zo gida aka dauke shi, ‘Yan bindigan sun tuntubi iyalinsa sun bukaci a kawo N100m domin su fito da shi.

Daga baya an rage kudin da suka tuntube su a waya a ranar Asabar, suka ce a aiko masu N50m.

Sarkin Gundiri ya fito

Labarin garkuwa da Nshe da Hassan ya zo ne jim kadan bayan an samu labarin cewa Mista Charles Dakat ya fito daga hannun ‘yan bindiga.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da Dakat wanda ke rike da kasar Gindiri a karamar hukumar Mangu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel